| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Takunkumin ECOWAS ya hana Nijar biyan bashin da ake bin ta
Bashin da ake bin Nijar ya karu zuwa Cfa biliyan 187.136 kwatankwancin dala miliyan 304 tun daga watan Yuli sakamakon juyin mulki da kuma dakatar da kasar daga kasuwannin hada-hadar kudaden kasashen yammacin Afirka.
Takunkumin ECOWAS ya hana Nijar biyan bashin da ake bin ta
Bashin da ake bin Nijar ya karu zuwa CFA biliyan 187.136 kwatankwancin dala miliyan 304 / Hoto:AFP  / Others

Hukumar da ke kula da basussuka ta yankin yammacin Afirka ta bayyana cewa takunkuman da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS da kungiyar hada-hadar kudaden ta yammacin Afirka suka kakaba wa Nijar sun taka rawa wajen hana kasar biyan basussukan da ake bin ta.

Bashin da ake bin Nijar ya karu zuwa Cfa biliyan 187.136 kwatankwancin dala miliyan 304 tun daga wata Yulin 2023 sakamakon yanayin juyin mullki da kuma matakin dakatar da ita daga kasuwannin hada-hadar kudaden Yammacin Afirka.

Hukumar kungiyar kasashen da ke amfani da kudaden Cfa ta UMOA Titres ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata,

Ta kara da cewa har yanzu Nijar ba ta biya bashin da ake bin ta na kudin ruwa kusan Cfa biliyan 2.464 ($4 m) ba.

''Wannan lamari na bashin kudin ya biyo bayan takunkumin da taron shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar tattalin arziki da hada- hadar kudaden Afirka ta yamma ya kakaba wa kasar Nijar," in ji hukumar.

ECOWAS da kungiyar hada-hadar kudaden yammacin Afirka sun dakatar da Nijar daga kasuwannin hada-hadar kudi na yankin da kuma babban bankin shiyyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a watan Yuli inda suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.

Kungiyar ta kakaba wa gwamnatin mulkin sojin Nijar takunkumai masu tsauri ciki har da hana ta amfani da kudaden ajiyar Nijar na kasashen ketare da ke bankin shiyyar tare da barazanar yin amfani da karfin soji domin maido da tsarin mulkin dimokuradiyya a kasar.

MAJIYA:Reuters
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai