| Hausa
DUNIYA
7 MINTI KARATU
Hanyoyin sadarwa sun katse gaba daya a Gaza saboda rashin fetur
Hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kaiwa ta sama da ta kasa a Gaza — wadanda suka shiga kwana na 41 — sun yi sanadin mutuwar Falasadinawa 11,500, ciki har da kananan yara 4,710 da mata 3,160, a cewar hukumomin Falasdinu.
Hanyoyin sadarwa sun katse gaba daya a Gaza saboda rashin fetur
Gaza / Others

Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023

1522 GMT —Hanyoyin sadarwa sun katse gaba daya a Gaza saboda rashin fetur

Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA, ya ce baki daya hanyoyin sadarwa sun katse a Zirin Gaza bayan ƙarancin man fetur da ake yi sakamakon mamaye yankin Falasdinawa da Isra'ila ta yi.

"Gaza ta sake shiga cikin yanayin katsewar hanyoyin sadarwa baki daya, kuma... saboda rashin man fetur ne, "in ji shugaban na UNRWA Philippe Lazzarini a wani taron manema labarai a Geneva.

Kamfanin sadarwa na Falasdinu Paltel ya kuma sanar da dakatar da aikin wayar salula da kuma intanet a duk fadin Gaza saboda rashin makamashi.

1358 GMT — An 'lalata' sashen kiwon lafiya a harin Asibitin Al Shifa na Isra'ila —Jami'i

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta ce wani harin da Isra'ila ta kai ya lalata wani sashen kiwon lafiya da kuma lalata wasu sassan biyu a babban asibitin Gaza, inda daruruwan majiyyata da ma'aikata da Falasdinawa da suka rasa matsugunansu ke samun mafaka.

Dakarun Isra'ila da suka shiga asibitin Al Shifa ranar Laraba sun "ruguza sashen daukar hoton ƙirji, tare da jefa bama-bamai a sassan ƴan ƙuna da na masu ciwon ƙoda," kamar yadda mai magana da ma'aikatar kiwon lafiya Ashraf al Qudra ya shaida wa AFP.

1152 GMT —Motocin buldoza na Isra'ila sun soma haka rami a Asibitin Al Shifa

Motocin buldoza na Isra'ila sun soma haka ramuka a karkashin kasa na Asibitin Al Shifa da ke Gaza, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

"Tankokin yaki sun fita daga cikin ginin, amma motocin buldoza na sojoji sun shiga cikinsa ta lambun da ke baya inda suka soma haka manyan ramuka," a cewar majiyar.

Ta kara da cewa motocin na buldoza sun rusa dukkan tantuna da katangun da ke asibitin.

"Dakarun Isra'ila sun yi kawanya a baki daya kewayen asibitin kuma suna far wa duk wanda ya yi yunkurin shiga ko fita," in ji majiyar.

0907 GMT — ‘Yan Isra’ila 7 sun jikkata a harbe-harben Gabashin Kudus: ‘Yan sanda

‘Yan Isra’ila 7 ne suka jikkata a wani harin harbe-harbe da aka kai Gabashin birnin Kudus, a cewar ‘yan sanda.

'Yan sanda sun ce an kai harin ne a kusa da wani shingen bincike da ke kudancin Gabashin birnin Kudus.

Ma’aikatar aikin ceto ta Magen David Adom ta ce daya daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin yanayi.

‘Yan sandan sun ce sun harbe wani tare da kawar da wasu mutane uku da ake zargi da hannu a harin.

0620 GMT — Isra'ila ta ki amincewa da kudurin MDD na tsagaita wuta

Ma'aikatar Harkokin Wajen Isra'ila ta yi watsi da kudurin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya amince a "tsagaita wuta" a Gaza.

A wata sanarwa da jaridar Haaretz ta wallafa, ta ambato ma'aikatar tana cewa "babu wata kafa ta tsagaita bude wuta" muddin kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta ci gaba da rike mutanen da ta yi garkuwa da su.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ranar Laraba ya amince da wani daftari wanda ya yi kira a "gaggauta tsagaita wuta" a fadin Gaza.

Kasashe goma sha biyu ne suka amince da kudurin wanda kasar Malta ta gabatar, yayin da Amurka da Birtaniya da Rasha suka kaurace wa kada kuri'a.

0400 GMT — An kashe wasu sojojin Isra'ila a Gaza

An kashe karin sojojin Isra'ila biyu a gumurzun da ake yi a Zirin Gaza, a cewar kafar watsa labarai ta gwamnatin Isra'ila KAN.

Kafar watsa labaran ta ambato wasu majiyoyi sojin kasar suna cewa an kuma jikkata wasu sojojin kasar biyu a fafatawar.

Hakan na nufin an kashe sojojin Isra'ila hamsin da daya tun 27 ga watan Oktoba.

0342 GMT — 'Yan Majalisar Dokoki 24 na jam'iyyar Democrat sun bukaci shugaban Amurka ya sa a tsagaita wuta a Gaza

'Yan majalisar wakilai ashirin da hudu na jam'iyyar Democrat ranar Laraba sun bayyana "matukar damuwa" game da hare-haren da Isra'ila take kaiwa a Gaza, sannan suka yi kira ga shugaban Amurka Joe Biden ya sa a tsagaita wuta.

A wasikar da suka aika wa Biden, 'yan majalisar, wadada suka hada da Alexandria Ocasio-Cortez da Betty McCollum, sun ce an "yi mummunar keta doka" kan kananan yara a Gaza.

Sun kara da cewa dole a tsagaita wuta idan ba haka ba Isra'ila za ta ci gaba da kashe fararen-hula kuma hakan zai jefa Amurka cikin yaki "mummuna kuma mara hikima" da za a yi a fadin Gabas ta Tsakiya.

0142 GMT — Samar da kasashe biyu ita ce mafita ga rikicin Isra'ila da Falasdinawa, in ji Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya bayyana wa Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa samar da kasashe biyu ita ce mafita kadai game da rikicin Isra'ila da Falasdinawa kuma sake mamaye Gaza zai kasance babban kuskure.

Biden ya shaida wa manema labarai cewa yana daukar dukkan matakan da suka dace bisa karfin ikon da yake da shi domin ganin an kubutar da mutanen da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su, sai dai ya ce ba ya nufin daukar matakin soji.

"Ba na so na yi gaban kaina a wannan lamari domin ban san abin da ya faru ba a awanni hudu da suka gabata, sai dai mun samu babban hadin kai daga kasar Qatar," in ji shi a yayin da aka tambaye shi game da ci-gaban da ake samu kan mutanen da aka yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktoba.

MAJIYA:AA, AFP, Reuters, TRT World
Rumbun Labarai
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Kasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha: Lavrov