| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
An rantsar da mambobin hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijar
Janar Abdourahamane Tiani wanda ya dare kan karagar mulkin Nijar bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli, ya rantsar da sabbin shugabannin hukumar yaki da cin hanci da rashawa a hukumance da kuma kotun jiha.
An rantsar da mambobin hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijar
An yada taron bikin rantsawar kai tsaye ta kafar talabijin na kasar ce ta watsa . Hoto: shafin X na Shugaban kasar Nijar  / Others

Shugaban Mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani wanda ya dare karagar mulkin kasar bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli, ya rantsar da shugabannin hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma kotun jiha na kasar a hukumance a ranar Alhamis.

Kafar talabijin na kasar ce ta watsa taron bikin rantsawar guda biyu kai tsaye.

Sabbin shugabannin hukumar da na kotun sun yi rantsuwar fara aiki a gaban shugaban mulkin sojin kasar wato Janar Abdourahamane Tiani.

Taron na zama karo na farko da shugaban ya taba bayyana a bainar jama'a tun bayan da ya jagoranci hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Manyan hafsoshin soji da mambobin gwamnati da sarakunan gargajiya da malaman addini da kuma jami’an diflomasiyyar kasashen waje ne suka halarci bikin rantsarwar a babban birnin kasar, Yamai.

Sabuwar kotun jihar za ta maye gurbin kotun sauraron kararrakin zabe da kuma ta majalisar dokokin jiha da aka rusa bayan juyin mulkin kasar.

A yanzu haka dai gwamnatin mulkin sojin ta bukaci ta mika mulki ga farar hula nan da shekaru uku masu zuwa, sai dai ba a kayyade ranar da za a gudanar da zabe ba.

Aikin hukumar yaki da cin hanci

Babban aikin hukumar yaki da cin hanci da rashawa shi ne kwato dukiyoyin al’umma da aka ƙwace ba bisa ƙa’ida ba.

Ma'aikatan hukumar sun ƙunshi alkalai da sojoji da jami’an ‘yan sanda da kuma wakilan al’umma.

Tiani ya yi alkawarin gudanar da taron tattaunawa na kasa, wanda zai taimaka wajen sanin ainihin lokacin da za a kwashe da kuma wa'adin mika mulki za su kasance.

Bazoum dai yana tsare a gidansa da ke tsakiyar fadar shugaban kasa tun bayan hambarar da shi.

Tun bayan juyin mulkin da kungiyar ECOWAS ta ƙaƙabawa Nijar takunkumin karya tattalin arziki, abin da ya janyo hauhawar farashin kayayyaki da kuma haifar da karancin wasu kayayyakin da suka hada da magunguna.

MAJIYA:AFP
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai