| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
NDLEA ta kama gawurtaccen mai safarar wiwi shekara bakwai bayan ya tsere daga gidan yari
An kama Ibrahim Momoh a karon farko a ranar 27 ga watan Nuwambar 2014 da tabar wiwi mai nauyin kilo 385.1 inda kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai da rabi a ranar 22 ga watan Yulin 2015.
NDLEA ta kama gawurtaccen mai safarar wiwi shekara bakwai bayan ya tsere daga gidan yari
An kama Ibrahim Bendel bayan an shafe shekara bakwai ana nemansa. / Hoto: NDLEA / Others

Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta kama wani gawurtaccen mai safarar miyagun kwayoyi wanda ya taba tserewa daga gidan yarin Kuje.

Hukumar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce jami’anta sun kama Ibrahim Momoh wanda aka fi sani da Ibrahim Bendel a maboyarsa da ke Filin Dabo da ke unguwar Dei-Dei a Abuja.

An kama Ibrahim Momoh a karon farko a ranar 27 ga watan Nuwambar 2014 da tabar wiwi mai nauyin kilo 385.1 inda kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai da rabi a ranar 22 ga watan Yulin 2015.

Sai dai Momoh din ya tsere daga gidan yarin na Kuje a ranar 16 ga watan Mayun 2016, kamar yadda hukumar ta NDLEA ta bayyana.

“Bayan samun bayanan sirri, NDLEA a ranar 20 ga watan Nuwambar 2022 ta kai samame dakin ajiye kayayyaki na Ibrahim Momoh wanda ya tsere daga gidan yari, inda aka gano manyan buhuna 81 na wiwi masu nauyin 1,278. “Dakin ajiye kayayyakin na a gonar kajinsa da ke Dei-Dei da ke Abuja,” in ji sanarwar.

Hukumar ta ce Momoh ba ya gonar a lokacin da suka kai samame gonar sai dai manajan gonar mai suna Richard Forson dan kasar Ghana wanda aka kama sannan aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu.

“An samu nasara a neman da ake yi wa gawurtaccen mai safarar kwayoyin a ranar 5 ga watan Nuwambar 2023 a lokacin da jami’an NDLEA suka sake kai samame a gonarsa da ke Filin Dabo inda aka kama shi da kilo 56.9 na wiwi da kuma gram 42.7 Na Diazepam," in ji NDLEA.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai