Shugaban kasar Turkiyya ya ziyarci kasar Aljeriya ana tsaka da rikicin Gaza

Ana sa ran shugabannin kasashen Turkiyya da Aljeriya za su tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da batutuwan da suka shafi yanki da na duniya, ciki har da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza

By trtafrikahau
Shugabannin kasashen biyu za su jagoranci taro na biyu na kwamitin hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Aljeriya.Hoto: AA / Others

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya karɓi baƙuncin takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a Algiers babban birnin kasar.

Erdogan da Tebboune sun fara ganawarsu a ranar Talata bayan wani bikin maraba da aka yi a fadar shugaban kasar Aljeriya

A yayin ziyarar, shugabannin biyu za su jagoranci taro na biyu na kwamitin hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Aljeriya.

A taron majalisar, za a tattauna matakan ƙara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Erdogan da Tebboune za su kuma yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi yankin da ma duniya baki daya, ciki har da hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza.