Gwamnati ta rage kudin wutar lantarki a Ghana
Wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar a kwanakin baya ya ce kasar Ghana ce ta farko a fannin samar da isashiyar wutar lantarki ga jama'arta a Afirka idan aka kwatanta da sauran kasashe masu arzikin makamashi irin su Nijeriya da Kenya.
Hukumar da ke sa ido kan biyan biyan kudaden wuta da ruwa da sauran kayan amfani a kasar Ghana ta rage kudin wutar da za a biya a kasar da kashi 1.52 cikin 100.
Sai dai karin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta PURC ta yi karin kudin da za a rinka biya na ruwa a kasar da kashi 0.34 a cikin 100 a rubu’i na karshe na shekarar 2023.
Kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito cewa wannan sabon gyaran da aka yi a farashin wuta da ruwa zai soma aiki ne daga 1 ga watan Disambar 2023 zuwa 29 ga watan Fabrairun 2024.
Sakamakon wannan karin da aka yi, masu zama a unguwannin marasa galiho za su soma biyan Cedi 0.6348 a duk kWh idan aka kwatanta da 0.6446 da suke biya a halin yanzu.
Sai kuma sauran jama’a za su rinka biyan Cedi 1.40 a duk kWh daga Cedi 1.42 da suke biya a baya.
Ga kuma masu amfani da ruwa a cikin gidaje, za su soma biyan Cedi 4.7401 a duk m3 daga 1 ga watan Disamba a maimakon 4.7239 da suke biya a halin yanzu.
Sai kuma wuraren da ba gidaje ba za su rinka biyan Cedi 14.19 a duk m3 a maimakon 14.1394 da uske biya, sai kuma wuraren kasuwanci za su rinka biyan Cedi 25.38 daga 25.2962 da suke biya.