| Hausa
WASANNI
2 MINTI KARATU
Tsohon kocin Ingila da Barcelona Terry Venables ya rasu
Tsohon kocin ya rasu yana da shekara 80, kamar yadda iyalansa suka tabbatar a ranar Lahadi.
Tsohon kocin Ingila da Barcelona Terry Venables ya rasu
Tsohon kocin ya rasu yana da shekara 80 da haihuwa. / Hoto: Getty Images / Others

Tsohon kocin Ingila Terry Venables ya rasu, kamar yadda wata sanarwa da iyalansa suka fitar a ranar Lahadi ta tabbatar.

Tsohon kocin ya rasu yana da shekara 80 kuma shi ya jagoranci tawagar kwallon kafa ta Ingila zuwa gasar Euro 96 inda har Ingilar ta kai zagayen kusa da na karshe.

Haka kuma tsohon kocin shi ya jagoranci Barcelona zuwa wasan karshe na Gasar Cin Kofin Turai a 1986. Muna matukar bakin ciki da rashin miji da uba nagari wanda ya rasu jiya bayan doguwar jinya,” in ji iyalansa.

“Za mu nemi a ba mu dama domin a wannan lokaci mai cike da bakin ciki don nuna alhinin rashin wannan mutum da muke kauna da muka yi sa'ar samu a rayuwarmu,” in ji iyalansa.

Baya ga Ingila da Barcelona, tsohon kocin ya jagoranci kungiyar Tottenham da Crystal Palace da Australiya.

Marigayin ya shahara tun a shekarun 1960 a lokacin da ya buga wa kungiyoyin Chelsea da Totteham da Queens Park Rangers wasa.

MAJIYA:AFP
Rumbun Labarai
Istanbul ta cika da ɗoki da karsashi gabanin wasan Galatasaray da Barcelona a Gasar Zakarun Turai
Hukumar ƙwallon ƙafar Portugal ta dakatar da Ronaldo daga buga wa ƙungiyar ƙasar wasa
Messi da 'yanwasan Argentina sun mana wulakanci, "sun hana mu jesi da yin hoto", in ji kocin Benin
Arda Guler ya tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid zuwa 2031
Ronaldo zai iya komawa tawagar Portugal idan yana so, in ji kocin ƙasar
Tirkashi: Real Madrid na so a ƙwace wa Barcelona kofuna 9, ta gabatar da ƙorafi mai shafi 50,000
Shugaban hukumar ƙwallo da kocin Portugal sun zauna don lallashin Ronaldo bayan ƙin saka shi a wasa
Barcelona ta fusata da Ancelotti kan raunin da Raphinha ya samu a wasan Brazil da Australia
An samu Manchester City da laifin keta dokokin kuɗi
Nijeriya da Ghana sun sha kashi a wasannin neman gurbin shiga Gasar AFCON ta 2027
Manyan kulob sun shirya wawason 'yanwasan Man City idan kotu ta kore ta daga Gasar Firimiya
Zidane ya yaba wa Turkiyya gabannin wasansa na farko a matsayin mai horar da tawagar Faransa
Taiwo ya maye gurbin Osimhen yayin da aka buɗe sansanin horaswa na Super Eagles
Kocin Super Eagles ya fitar da sunayen ‘yanwasan da za su buga wasanni a Satumba da Oktoba
Messi ya ci ƙwallonsa ta 100 a Inter Miami yayin da suka lashe Kofin Campeones
Mbappe ya ce ya ƙi sa rigar Ceuta yadda ya kamata ne don tausaya wa baƙin haure 'yan Morocco
Messi na shirin buga wa Argentina wasansa na ƙarshe
Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar