Wani ɗan Nijeriya mai suna Usama Murtala ya rasu jim kaɗan bayan an sake shi daga tsarewa a ƙasar Côte d'Ivoire, inda shi da wasu matasa biyar 'yan Nijeriya suka shafe kusan shekara guda a tsare ba tare da an gurfanar da su a kotu ko kuma an tuhume su da wani laifi ba.
Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Ojukwu ce ta bayyana hakan a shafinta na X ranar Talata, inda ta ce matasan sun yi tafiya ta mota daga Jihar Sokoto zuwa birnin Abidjan domin gudanar da kasuwancin saye da sayar da kayan gyaran wayoyin hannu.
A cewarta, an kama su ne a ƙarƙashin wasu yanayi da ba su bayyana ba, sannan aka tsare su a gidan yarin MACA da ke Abidjan.
Ministar ta ce ba a sanar da ofishin jakadancin Nijeriya da ke Côte d'Ivoire game da kama su ba, lamarin da ya hana su samun taimakon ofishin jakadanci na tsawon watanni.
NiDCOM ta ce an sanar da ita halin da matasan ke ciki ne a watan Afrilu na shekarar 2026. Bayan haka ne ta tuntubi ofishin jakadancin Nijeriya da ke Abidjan, inda ta gano cewa hukumomin Côte d'Ivoire ba su taɓa sanar da jakadancin game da kama mutanen ba.
Bayan tattaunawa da kuma matakan diflomasiyya da ofishin jakadancin Nijeriya da Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya suka ɗauka, an samu nasarar tabbatar da sakin matasan.
Sai dai a lokacin da aka sake Usama Murtala, jikinsa ya riga ya tsananta sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita yayin da yake tsare.
Duk da ƙoƙarin jami'an jakadancin Nijeriya na garzayawa da shi wani asibitin kula da masu fama da matsananciyar rashin lafiya, ya rasu washegarin ranar da aka sake shi.
Rahotanni sun ce iyalansa da ke Sokoto suna cikin shirye-shiryen tarbarsa a gida, ba tare da sun san cewa halin da yake ciki ya yi muni ba.
Bisa buƙatar iyalansa, an binne Usama a wata makabarta da ke wajen birnin Abidjan bisa koyarwar addinin Musulunci, tare da halartar jami'an ofishin jakadancin Nijeriya da kuma abokan zamansa da aka tsare tare.
Ana sa ran sauran 'yan Nijeriyar biyar da aka saki—Aliyu Malami, Nasiru Umar, Shamsu Abubakar, Sa'adu Bello da Lyman Mohammed—za su dawo Najeriya nan ba da jimawa ba, inda jami'an gwamnati za su tarbe su.
Minista Bianca ta bayyana mutuwar Usama a matsayin babban abin takaici da ke nuna irin ƙalubalen da matasa da dama ke fuskanta yayin da suke barin ƙasarsu domin neman ingantacciyar rayuwa a ƙasashen waje.
Ta ce da yawa daga cikin 'yan Nijeriya da ake tsare da su a ƙasashen waje na shiga mawuyacin hali saboda rashin sanin tsarin shari'ar ƙasashen da suka je da kuma rashin samun isasshen tallafi.
Ta kuma bayyana cewa Nijeriya za ta bi diddigin lamarin tare da hukumomin Côte d'Ivoire domin neman ƙarin bayani kan mutuwar Usama, yayin da ta bayyana labarinsa a matsayin wani abin tunatarwa kan irin haɗurran da ke tattare da tafiyar neman ingantacciyar rayuwa a ƙasashen waje.














