Rundunar Kare Juyin Juya-Hali ta Iran (IRGC) ta ce dakarun sojin ruwanta sun kai hari kan wani jirgin ruwa mai suna MSC Sariska da makami mai linzami a wani abin da ta bayyana a matsayin wani "aikin ramuwar gayya" biyo bayan wani abin da ta kira harin Amurka a kan wani jirgin ruwan Iran a tekun Oman.
Wata sanarwa da kafar watsa labaran ƙasar Iran IRIB ta samu ranar Litinin ta ce harin ya zo ne bayan abin da IRGC ta kira wani "hari na tsokana" da sojin Amurka ta kai kan wani jirgin ruwan Iran mai suna Lian Star a tekun Oman.
Sanarwar ta yi iƙirarin cewa jirgin mai suna MSC Sariska mallakin abin da ta kira "abokan gaba Amurka da masu kaifin kishin kafa ƙasar Yahudawa."
Rundunar ta ce an kai hari kan jirgin ruwan ne a wani ɓangare na wani "aiki na ramuwar gayya" da dakarun sojin ruwanta suka kai.
Ba ta ba da cikakken bayani game da ta’adi da ta yi wa jirgin ruwan ko kuma yiwuwar mace-mace ba.
Rundunar IRGC ta yi gargaɗin cewa duk wani ƙarin matakin da dakarun Amurka za su ɗauka a yankin zai fuskanci wani “martani mai ƙarfi."
"Duk wani mataki na tsangwama da sojin Amurka ta yi a yankin zai fuskanci martani mai ƙarfi," in ji sanarwar.
“Bayyanannun ƙeta haddi”
Daga farko, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce Tehran ta ɗaura wa Amurka laifin yadda Isra’ila ke ƙeta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, tana mai gargaɗn cewa Tehran za ta kare muradunta “a duk inda yin hakan ya zama wajibi.”
Ma’aikatar ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta ta ranar 8 ga watan Afrilu ta dakatar da abin da ta kira yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaƙaba a duka ɓangarori, ciki har da Lebanon.
Ta ce tun lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki , Amurka tana ta aikata “bayyanannun ƙeta haddi” kan yarjejeniyar, ciki har da yadda take katsalandan a harkar jigilar kayayyaki na kasuwanci na jiragen ruwan Iran.

![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=720&format=webp&quality=80)
![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=128&format=webp&quality=80)







