Gwamnatin Falasdinu da ke Gaza ta dora alhakin "laifukan yakin da Isra'ila take ci gaba da aikatawa" a kan kasashen duniya, a yayin da dakarun Isra'ila suka ci gaba da kaddamar da hare-hare a Gaza bayan karewar wa'adin yarjejeniyar tsagaita.
"Rundunar sojin Isra'ila da ke mamaya ta sake kaddamar da yaki mai muni a kan al'ummar Falasdinu da ke Zirin Gaza,” a cewar wata sanarwa da ofishin watsa labarai na gwamnati da ke Gaza ya fitar ranar Juma'a da safe.
Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare a gidaje da dama da kuma kan fararen-hula a Gaza, in ji ofishin na watsa labarai, inda ya jaddada cewa: “Kasashen duniya ne za su dauki alhakin laifukan yakin da Isra'ila ke ci gaba da aikatawa a Zirin Gaza.”
Hukumomin lafiya a Gaza sun bayyana cewa luguden wutar da Isra'ila take ci daga da yi a yau ya kashe Falasdinawa 32.
“Kasashen duniya, musamman Amurka da shugabanta Joe Biden da Sakataren Harkokin Waje Antony Blinken, su ne da alhakin laifukan mamaya da na yakin da Isra'ila take aikawa a kan fararen-hula da kananan yara da mata a Gaza,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa: “An keta dokokin yaki da na kasashen duniya game da jinkai. Kasashen duniya sun bai wa Isra'ila damar ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza.”
Hare-hare ta sama
“Al'ummar Falasdinu suna da 'yancin kare kansu ta dukkan wata hanya, domin samun 'yanci da mutunci, domin kafa kasar Falasdinawa mai hedkwata a birnin Kudus kamar yadda dokokin duniya suka tanada, da kuma kawar da masu mamaya daga kasarsu,” a cewar sanarwar.
Jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare a yankuna daban-daban da ke Gaza da sanyin safiyar Juma'a, kamar yadda masu aiko wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu da ke yankuna suka tabbatar.
Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakanin Isra'ila da Hamas ranar 24 ga watan Nuwamba ta kare ranar Juma'a da safe.
Daga nan ne Isra'ila ta kaddamar da luguden wuta ta sama a gabashin Gaza.















