| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
An bayar da shawarar kafa tarayyar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso
Ministan Harkokin Wajen Mali Abdoulaye Diop ya ce za su mika shawarar ga shugabannin kasashen, wadanda za su gana a Bamako a wani lokaci da ba a bayyana ba.
An bayar da shawarar kafa tarayyar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso
Kasashen uku na karkashin mulkin soji inda a Mali da Burkina sojoji suka kwace mulki a 2020 da 2022, sannan a Nijar sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata./Hoto: Ofishin shugaban kasar Jamhuriyar Nijar / Others

Ministocin kasashen wajen Burkina Faso da Mali da Nijar ranar Juma’a sun bayar da shawarar kirkiro tarayyar kasashen uku a wani bangare na hada kan kasahen don su zama a dunkule wuri daya.

Dukkan kasashen uku na karkashin mulkin soji inda a Mali da Burkina sojoji suka kwace mulki a 2020 da 2022, sannan a Nijar sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.

Tuni dama suka kirkiri wata kungiya mai suna Alliance of Sahel States da zummar karfafa tsaro da bunkasa tattalin arziki a tsakaninsu.

A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan kammala taron kwana biyu a Bamako babban birnin Mali, ministocin harkokin wajen kasashen uku sun bayyana cewa “akwai babbar dama ta zaman lafiya da kwanciyar hankali da karfafa diflomasiyya da bunkasa tattalin arziki idan aka yaukaka dangantaka da alaka ta siyasa”.

Labari mai alaka: Sahel Alliance: Nijar, Burkina Faso da Mali sun kulla kawance

"Ministocin... bisa burinmu na kasancewa tarayya da za ta hada Burkina, Mali da Nijar muna bayar da shawarar kirkiro tarayya ta shugabannin kasashen kungiyar Alliance of Sahel States,” in ji sanarwar.

Ministan Harkokin Wajen Mali Abdoulaye Diop ya ce za su mika shawarar ga shugabannin kasashen, wadanda za su gana a Bamako a wani lokaci da ba a fayyace ba.

Kazalika gwamnatocin sojin kasashen uku sun hada wata gamayya da za ta tunkari duk wani matsin lamba daga kasashen waje game da komawarsu kan turbar dimokuradiyya da kuma magance hare-haren masu ikirarin jihadi da ke addabar kasashen.

MAJIYA:AFP
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai