| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Shugaban kamfanin BUA Abdul Samad ya ki karbar mukamin da APC ta ba shi
Jam'iyyar APC mai mulki ta saka Abdul Samad Rabiu da Dahiru Mangal da A. A Rano da wasu hamshakan 'yan kasuwa na Nijeriya a cikin kwamitin kudi na jam'iyyar.
Shugaban kamfanin BUA Abdul Samad ya ki karbar mukamin da APC ta ba shi
Kamfanin BUA ya yi godiya ga APC bisa wannan karamcin sai dai ya ce babu ruwan kamfanin ko shugaban kamfanin da siyasa./ Hoto: Bua Cement Plc / Others

Shugaban kamfanin BUA a Nijeriya Abdul Samad Rabiu ya yi watsi da mukamin da aka ba shi na mamba a kwamitin kudi na Jam’iyyar APC.

Abdul Samad din ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da kamfaninsa na BUA ya fitar a shafin X inda ya ce babu wanda ya tuntube shi kafin a ba shi wannan mukamin.

A ranar Juma’a ne Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da sunayen mambobin kwamitocinta wadanda suka hada da na gudanarwa da kudi da watsa labarai da harkokin gwamnati da sasanci.

A cikin kwamitin na kudi, baya ga Abdul Samad, akwai sauran hamshakan ‘yan kasuwa na Nijeriya da ke cikin kwamitin irin su Dahiru Mangal da A. A Rano da Alhaji Mohammed Indimi.

“Muna mika godiyar mu ga jam'iyyar APC bisa la'akari da shugabanmu kan irin wannan gagarumin aiki,” in ji sanarwar.

“Wannan karramawa ta nuna kokarinsa, da kuma na kamfanin BUA, wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasarmu Nijeriya. Sai dai yana da kyau a san da cewa shugabanmu, Abdul Samad Rabiu da kamfanin BUA ba su shiga siyasa tsawon shekaru.

“Wannan tsarin yana da nasaba da yanayin kasuwancinmu kuma ya yi daidai da yadda Rabiu ya mayar da hankali wajen inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar shirye-shiryen kungiyar BUA da kokarin taimakon jama'a ta hanyar shirin ASR Africa.

"Dangane da wannan, muna sanar da ‘yan jarida da abokan aikinmu da masu ruwa da tsaki, da sauran jama'a cewa Rabiu ya yanke shawarar kin amincewa da wannan mukamin,” in ji sanarwar.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Mali ta ɗaure jami'in diflomasiyyar Faransa shekara 20 a gidan yari kan zargin neman haddasa rikici
Fafutukar samar da kiwon lafiyar bai-ɗaya a Afirka
An yi wa jagoran 'yan adawa na Guinea Bissau ɗaurin talala
Ƙishirwa ta kashe mutum 49 a saharar Nijar bayan motarsu ta lalace
Mali ta haramta hawa babura a wajen birane saboda hare-haren ta'addanci
Tawagar kwallon DRC na neman abokiyar karawa bayan Sifaniya ta fasa buga wasa da su saboda Ebola
'Yan Nijeriya da Mozambique da Laberiya na cikin mutum  21 da gobarar otel ta kashe a New Delhi
Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani ya fara ziyarar aiki a Turkiyya
Nijar da Benin sun ƙaddamar da kwamitin da zai sa ido kan iyakokin ƙasashen biyu
Manyan attajiran Afirka da kuma nauyin talaucin da nahiyar ke fama da shi
Malawi za ta kwashe 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu saboda matsalar rikicin ƙyamar baƙi
Dalibai tara sun gurfana a gaban kotu kan tayar da gobara a wata makaranta a Kenya
Mutane da yawa sun fito da wuri don kaɗa kuri'a a babban zaben Habasha
Shugaban WHO ya ziyarci cibiyar Ebola yayin da cutar ke ƙara ƙamari
Amurka ta aike wa Nijar kayan aikin soja da darajarsu ta kai dala miliyan 2.3 duk da takun-saƙa
Ɗalibai 16 sun rasu sakamakon gobara a wata makarantar 'yanmata a Kenya
Ghana ta kwashe 'yan ƙasarta 300 daga Afirka ta kudu yayin da ake zanga-zanga kan baƙin haure
Mutane uku sun mutu bayan motar fasinja ta yi karo da giwa a gandun dajin Uganda
Shugaban Senegal Faye ya naɗa sabon firaminista da zai maye gurbin Sonko
Adadin mutanen da Ebola ta kashe a Jamuhuriyar Kongo ya wuce 200