| Hausa
DUNIYA
6 MINTI KARATU
Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 700 a kwana guda a Gaza
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 58 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falaadinawa fiye da 15,207, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 40,000 sun jikkata.
Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 700 a kwana guda a Gaza
The Israeli attack includes a targeted strike by Israeli fighter jets on the "Holy Family school" in Gaza City, where many displaced people are seeking refuge. / Photo: AA / AA

1533 GMT — Isra’ila ta bayar da umarnin rushe gidan limamin Masallacin Al-Aqsa Sheikh Ekrima Sabri

Dakarun Isra’ila a ranar Lahadi sun kai samame unguwar Sawaneh da ke Gabashin Birnin Kudus da Isra’ila ta mamaye, inda suka yi ikirarin cewa wasu rukunin gidaje daga ciki har da gidan limamin masallacin Al-Aqsa, Sheikh Ekrima Sabri, ba a gina shi bisa ka’ida ba tare da bayar da umarnin rushe ginin.

“Dumbin dakarun ‘yan sanda da na leken asiri na Isra’ila suka kai samame ginin, daga ciki har da wurin da Sheikh Sabri mai shekara 85 yake zama a unguwar Sawaneh da ke Gabashin Birnin Kudus a ranar Lahadi da safe”, kamar yadda wadanda suka shaida lamarin suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa an gudanar da ginin shekaru da dama kuma yana dauke da Falasdinawa sama da 100 da gidaje 18

1420 GMT — Sojojin Isra'ila sun kama kusan Falasdinawa 60 a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Sojojin Isra’ila sun kama kusan Falasdinawa 60 a Gabar Yamma da Kogin Jordan, daga ciki har da mata biyar ‘yan jami’ia.

Sanarwar hadin gwiwa daga hukumar da ke kula da fursunoni da kuma kungiyar Palestinian Prisoner Club ce ta tabbatar da hakan.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da dare zuwa wayar garin Lahadi wanda hakan ya kawo jimlar adadin wadanda Isra’ilar ta kama a Gabar Yamma da Kogin Jordan zuwa 3,480 tun daga 7 ga watan Oktoba.

1345 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 700 a kwana guda a Gaza

Ofishin watsa labarai na Falasdinu a Gaza ya bayar da rahoton cewa hare-hare ta sama da Isra’ila ke kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar sama da mutum 700 a sa’o’i 24 da suka gabata.

Makarantar “Holy Family” wadda ke kasancewa a matsayin mafaka ga wadanda suka rasa muhallansu, ta zama daya daga cikin wuraren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa hari a birnin.

A Gabar Yamma da Kogin Jordan kuwa, Isra’ila ta bayar da umarnin rushe wani gini a unguwar Al Sawana da ke Gabashin Birnin Kudus wanda a ginin ne mai wa’azi a Masallacin Al Aqsa Sheikh Ikrimah Sabri yake tare da wasu iyalai.

0426 GMT — WHO ta bukaci a 'tsagaita wuta' a hare-haren Gaza

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana matukar kaduwa game da luguden wutar da Isra'ila take yi a Gaza.

Tawagar WHO da ke yankin ta ziyarci Asibitin Nassar da ke kudancin Gaza ranar Asabar, inda ta bayyana mawuyacin halin da mutane suke ciki.

Asibitin, wanda mutane suke tururuwar zuwa domin kula da lafiyarsu, yana aiki fiye da sau uku na yadda ya kamata abin da ya jefa shi cikin mawuyacin hali.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya wallafa sako a shafinsa na X inda ya bayyana mawuyacin halin da ake ciki a yankin, yana mai cewa fiye da "majiyyata 1,000 ne suke cikin asibit — adadin da ya zarta yadda ya kamata ya yi aiki har sau 3. Mutane da yawa na neman matsuguni a asibitin, inda suka cika shi makil."

Asibitin Nassar ya yi cikar da ba zai iya kula da marasa lafiya, inda yanzu ake kwantar da marasa lafiya a dandarin kasa inda suke cikin azaba.

0444 GMT — Isra'ila ta kashe kananan yara da mata a sabbin hare-haren da ta kai Gaza

Jiragen yakin Isra'ila sun kai jerin hare-hare a sassa dabna-daban na Gaza, inda suka kashe mutane da dama ciki har da mata da kananan yara, kamar yadda Ma'aikatar Cikin Gida ta yankin ta bayyana.

Hare-haren sun fi mayar da hankali ne a al Burij, Dier al Balah, da kuma wasu yankuna da ke gabashin Rafah.

Alkaluman mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza sun karu zuwa 15,207, sannan wadanda suka jikkata sun zarta 40,652. Jami'ai sun yi amannar cewa dubban gawawwaki na binne a cikin baraguzan gine-gine sakamakon hare-haren Isra'ila.

Kazalika, Isra'ila ta kaddamar da jerin hare-hare ta sama a Gabar Yamma da Kogin Jordan, abin da ya kara tayar da hankula a yankin.

A unguwar Qalqilya, dakarun Isra'ila sun kashe wani matashi dan shekara 21 sannan suka jikkata wasu mutane da dama. Hakan ya sa an sanya ayyana gudanar da gagarumar zanga-zanga a Qalqilya, abin da ya tayar da jijiyoyin wuya a yankin na Falasdinu.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Kasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha: Lavrov