| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
Turkiyya ta kwashe 'yan kasarta daga Gaza a yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta
Jami'an Ma'aikatar Harkokin Waje Turkiyya da na Hukumar Kiyaye Aukuwar Bala'i ne suka tarbi Turkawan da suka dawo daga Gaza a filin jirgin saman Istanbul.
Turkiyya ta kwashe 'yan kasarta daga Gaza a yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta
Jirgin saman Turkish Airlines dauke da 'yan kasar Turkiyys 142 ya isa Filin Jirgin Saman Istanbul . / Hoto: AA / Others

'Yan kasar Turkiyya da iyalansu wadanda aka kwaso daga Gaza sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa yankin sun isa Istanbul daga Masar.

Jirgin saman Turkish Airlines dauke da 'yan kasar Turkiyys 142 wadanda suka tsallaka Masar ta Mashigar Rafah sun sauka a filin jirgin saman Istanbul Dda sanyin safiyar Litinin bayan ya taso daga filin jirgin saman kasa da kasa na birnin Alkahira.

Jami'an Ma'aikatar Harkokin Waje Turkiyya da na Hukumar Kiyaye Aukuwar Bala'i (AFDA) ne suka tarbe su.

Wasu daga cikinsu sun yi ta hawaye a yayin da suka sauka daga jirgi.

Ranar 19 ga watan Nuwamba, Turkiyya ta kwaso 'yan kasarta 42 daga Gaza.

Isra'ila ta ci gaba da kai are-hare Gaza ranar Juma'ar da ta gabata bayan karewar wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar Hamas ta Falasdinawa.

Hare-haren da ta kaddamar ranar 7 ga watan Oktoba sun kashe Falasdinawa akalla 15,500, galibinsu kananan yara da mata bayan harin ba-zata da Hamas ta kai mata.

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Kasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha: Lavrov
Ƙanwar Kim Jong-un ta ce 'wawaye' ne kawai ke tunanin Koriya ta Arewa za ta miƙa makaman nukiliyarta
Taliban na neman ƙulla dangantaka da Amurka da sharaɗin a duba illolin yaƙin Afghanistan
Wuta za ku je idan ba ku jefa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisa ba, in ji Trump ga 'yan Republican
Shekaru 25 bayan 9/11, Amurkawa na tsoron ta’addancin cikin gida fiye da barazanar hari daga waje
Turkiyya da kasashe 7 sun yaba wa Birtaniya kan hana kawo kaya daga haramtattun mazaunan Isra'ilawa
An samu sojojin Jamus da laifuka kusan 2,000 da suka shafi cin zarafi ciki har da lalata da yara
Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin kafa rundunar sojin ruwa mai amfani da makaman nukiliya
Faɗaɗa Yarjejeniyar Makka: Me Bangladesh za ta iya kawo wa ƙawancen?
Kotu a Las Vegas ta samu tsohon jagoran 'yandaba Duane 'Keffe D' Davis da laifi a kisan Tupac Shakur
Cizon sauron da suka shiga Jamus ta jirgin sama ya kashe ma'aikatan filin jirgi biyu
Tsananin zafi ya yi ajalin mutane 15,800 a Jamus a bazarar bana
Shugaban hukumar leƙen asiri ta Rasha ya tabbatar da ganawa da Shugaban CIA a Moscow
Ambaliya da zaftarewar ƙasa a Nepal sun yi ajalin gommai da ɓatar da ɗaruruwa a kusa da iyakar China
Trump ya gabatar da yarjejeniyar shekaru 30 ta haɗin gwiwar nukiliyar Saudiyya ga Majalisar Amurka
Mummunar guguwa ta katse wutar lantarki a gidaje 26,000 a kudu maso-gabashin Faransa