| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 MINTI KARATU
Kamfanin intanet na Starlink na aiki ba bisa ka’ida ba a Ghana — Hukumar NCA
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta ce ba ta bai wa kamfanin Starlink lasisi ba, sannan ba ta amince da duk wasu na’urori da yake samarwa ba.
Kamfanin intanet na Starlink na aiki ba bisa ka’ida ba a Ghana — Hukumar NCA
Kamfanin wanda mallakin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya Elon Musk ne, yana samar da intanet hanyar amfani da tauraron dan'adam da ke karkashin kamfanin SpaceX. / Photo: Reuters / Reuters

Hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa a kasar Ghana (NCA) ta ce kamfanin samar da intanet na Starlink yana aikace-aikace a cikin kasar ne ba bisa ka’idar doka ba.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta ce ba ta bai wa kamfanin Starlink lasisi ba, sannan ba ta amince da duk wasu na’urori da kamfanin ke samarwa ba.

Kamfanin wanda mallakin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya Elon Musk ne, yana samar da intanet hanyar amfani da tauraron dan'adam da ke karkashin kamfanin SpaceX.

Hakan yana nufin duk wani kamfani da ke sayar da kayayyakin kamfanin Starlink ko samar da intanet ta hanyar amfani da kamfanin Starlink yana sani cewa hakan ya taka dokar hukumar NCA, in ji sanarwar.

Kazalika hukumar ta gargadi al’ummar kasar da kamfanoni kan sayan duk wata na’ura ko yin hulda da kamfanin Starlink.

Sai dai a shafin intanet din Starlink, kamfanin ya bayyana cewa yana shirin samar da intanet a watanni na kusa da karshen 2024 a Ghana. Sai dai ya ce hakan ya dogara ne kan amincewar hukumomin kasar.

Akwai wasu ’yan kasuwa a kasar da ke sayar da kayayyakin kamfanin a Ghana, inda rahotanni ke cewa suna cajar GH¢1,100 zuwa GH¢18,000 daga masu amfani da intanet a kowane wata.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Kotun Kenya ta ce a dakatar da aikin Matatar Mai ta Dangote ta dala biliyan 16
Dangote na shirin zuba jarin $10bn don shawo kan matsalar wutar lantarki a Nijeriya
Amurka ta ƙulla yarjejeniyar $414m kan aikin haƙar uranium a Nijar
Matatar Dangote ta sayar da hannayen-jarin fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan ƙaddamarwa
Matatar Dangote za ta buɗe sayar da hannayen-jari na Naira tiriliyan 2.15
Apple ya gabatar da iPhone Duo, wayarsa ta farko da ake rufewa
Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama'a
Uganda ta sanar da samun raguwar kaso 15% a hada-hadar fitar da kofi zuwa ƙasashen waje
Zuba jari a ɓangaren makamashi na Nijeriya na iya ƙaruwa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA
Matatar Dangote ta Nijeriya za ta fara sayar da hannayen jari a karon farko nan da ‘yan kwanaki
Shirin bankin da ba ya karɓar ruwa ba don tallata wani addini ba ne – Gwamnan Babban Bankin Ghana
Trump ya soki Canada kan haraji cikin rigimar cinikayyar da Amurka ke yi da ƙasar
Kayan da Turkiyya ta fitar zuwa Afirka a 2026 sun haura na dala biliyan 13
Kuɗin Ghana ya koma fuskantar matsi, na Uganda na farfaɗowa, na Nijeriya zai iya sauyawa kaɗan
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Matatar Dangote ta fitar da tan fiye da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli - Rahoto
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
A lokacin da cututtuka suka tsallaka iyaka: Manoman Afirka na neman sabbin matakan kariya