| Hausa
TURKIYYA
3 MINTI KARATU
Kwamitin Tsaro na MDD ya koma bayar da kariya ga Isra'ila: Shugaba Erdogan
“Mun cire rai da yanke tsammani da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya,” in ji Shugaba Erdogan inda ya kara da cewa "masu kashe mutane a Gaza za su girbi abin da suka shuka ko ba dade ko ba jima".
Kwamitin Tsaro na MDD ya koma bayar da kariya ga Isra'ila: Shugaba Erdogan
Akwai yiwuwar samar da duniya mai adalci, sai dai ba tare da Amurka ba saboda tana tare da Isra’ila, in ji shugaban. / Hoto: AA       / Others

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kara jaddada bukatar yin garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya bayan Amurka ta yi fatali da kudurin da aka gabatar ga kwamitin wanda zai bayar da dama a tsagaita wuta a hare-haren da Isra'ila take kai wa Gaza.

“Sakamakon watsi da Amurka ta yi da kudirin, ba a cimma wata matsaya ba. Yana da kyau a yi garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya,” kamar yadda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a wani jawabi da ya yi a ranar Asabar a taron Ranar Kare Hakkin Bil’adama ta Duniya wanda aka gudanar a birnin Santambul.

“Mun cire rai da yanke tsammani da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya,” in ji shi. “ Tun daga 7 ga watan Oktoba, kwamitin tsaron wanda aikinsa shi ne samar da zaman lafiya ya koma ba Isra’ila kariya.”

Isra’ila ta koma kai hare-hare ba kakkautawa kan Gaza tun daga 1 ga watan Disamba bayan an shafe mako guda ana morar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Falasdinu.

Kusan Falasdinawa 17,500 aka kashe a Gaza da aka yi wa kawanya a hare-hare ta sama da kasa tun bayan kaddamar da harin a ranar 7 ga watan Oktoba.

'Masu kashe mutane a Gaza za su girbi abin da suka shuka'

Erdogan ya jaddada cewa gwamnatin Isra’ila wadda ke samun cikakken goyon bayan Kasashen Yamma na gudanar da zalunci da kisan kiyashi a Gaza wanda ke kunyata bil’adama baki daya.

Ya kara jaddada cewa masu kashe mutane a Gaza za su girbi abin da suka shuka kan take hakkin bil adama da suka yi ko ba dade ko ba jima.

Ya bayyana cewa akwai yiwuwar samar da duniya mai adalci, sai dai ba tare da Amurka ba saboda tana tare da Isra’ila.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Kamfanin Fergani na Turkiyya ya tura tauraron ɗan'adam na gwaji na 6 sararin samaniya
Turkiyya, Qatar da Pakistan da Indonesia za su sanya hannu kan yarjejeniyar masana'antar tsaro
Antalya ya karɓi masu yawon buɗe ido miliyan 14 daga ƙasashen waje duk da ƙalubalen duniya
Spain na shirin sayen jirgin horar da mayaka na Hurjet kirar Turkiyya guda 15: Shugaban TAI
Turkiyya ta haramta wa shafukan sada zumunta yi wa 'yan ƙasa da shekara 15 rijista
Yarjejeniyar tsaro ta Makka ba ta ba da izinin kai hari kan ƙasashe ba - Turkiyya
Turkiyya ta yi wa Nijeriya ta’aziyya kan hatsarin jirgin soji
Shelar Antalya da Turkiyya ke jagoranta ta haɗa ƙasashe 21 a haɗin kan lumana kan sararin samaniya
Emine Erdoğan ta jagoranci kiran matan shugabannin duniya na son MDD tai tsarin kare yara a intanet
Turkiyya za ta ci gaba da magana kan Falasɗinawa: Erdogan
Zauren kotu ya dace da masu aikata laifukan yaƙi ba zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ba: Erdogan
Jami’an Sojin Ruwa 30 na Saudiyya sun kammala karɓar horo a kamfanin tsaron Turkiyya, Baykar
Yadda Turkiyya ke taimaka wa Iraƙi wajen isar da albarkatun manta zuwa kasuwannin ƙasa da ƙasa
An wallafa jawabin Shugaba Erdogan na UNGA-81 a matsayin littafi cikin harsuna uku
Shugaban Turkiyya Erdogan ya buƙaci haɗin ƙan Musulmai, ya soki nuna wariya
Emine Erdogan ta buƙaci a rabu da ‘al’adar jefar da kaya' a koma ga tsarin sabuntawa
Erdogan ya yi kira da a gyara MƊD, ya nemi a soke ikon kujerar na-ƙi
Abincin Afirka daga Turkiyya
Shugaba Erdogan na Turkiyya ya tafi New York taron Majalisar Dinkin Duniya
'Turkiyya za ta duba buƙatun Saudiyya ƙarƙashin yarjejeniyar Makkah yayin da Houthi ke kai hari'