Isra'ila ta ce an kashe mata sojoji 425 da raunata 1,593 tun daga 7 ga watan Oktoba
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe sama da wata biyu tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 17,700, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 48,780 suna karkashin baraguzan gine-gine inda ake fargabar sun mutu.
1255 GMT — Isra'ila ta ce an kashe mata sojoji 425 da raunata 1,593 tun daga 7 ga watan Oktoba
Rundunar sojin Isra’ila a ranar Lahadi ta sanar da cewa tun bayan soma yaki tsakaninta da Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, ta rasa sojojinta 425.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta bayyana cewa sojojin sun hada da 97 wadanda aka kashe tun bayan da Isra’ilar ta kara fadada hare-hare ta kasa da take kaiwa a Gaza tun daga 27 ga watan Oktoba.
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa akwai sojojin Isra’ila 1,593 da suka samu rauni tun bayan soma wannan yakin.
0239 GMT — Dakarun Isra'ila sun kutsa kudancin Gaza, kungiyoyin ba da agaji sun yi 'gargadi'
Dakarun Isra'ila sun kutsa kudancin Gaza, inda dubban fararen-hula suka tsere domin neman mafaka daga luguden wutar Isra'ila da kuma gumurzu tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas mai fafatukar kare hakkin Falasdinawa.
Kungiyoyin bayar da agaji sun yi kakkausan gargadi game da "matsalar rashin jinkai" da ake fama da ita a Falasdinu, suna masu cewa yankin yana dab da fadawa cikin yunwa da cututtuka.
Hamas ta ce Isra'ila ta kaddamar da jerin "manyan hare-hare" a Khan Younis da kuma hanyar da ta hada birnin da Mashigar Rafah, a kusa da kan iyaka da Masar.
Wani wakilin AFP ya bayar da labari kan luguden wutar ya mamaye kudancin Gaza da sanyin safiyar Lahadi.
0000 GMT — Hamas ta yi maraba da matakin Houthi na hana jiragen ruwan Isra'ila wucewa ta Bahar Maliya
Kungiyar Hamas da ke fafutukar kare hakkin Falasdinawa ta yi maraba da sanarwar da kungiyar Houthi ta kasar Yemen wadda Iran ke marawa baya ta fitar ranar Lahadi da ke cewa za ta hana hana jiragen ruwan Isra'ila wucewa ta Bahar Maliya.
Wata sanarwa da Hamas ta fitar ta jawo hankali game da sanarwar ta Houthi wadda ke cewa: "Idan ba a bari an shigar da kayan bukatu, ciki har da abinci da magunguna, zuwa Gaza ba, za a hana jiragen Isra'ika wucewa ta Bahar Maliya ko da kuwa na kowacce kasa ne."
Kungiyar ta yi jinjina game da wannan "mataki na rashin tsoro" da aka dauka kan hare-haren da aka kwashe fiye da wata biyu ana kaiwa Gaza sannan ta yi kira ga kasashen Larabawa da na Musulmai su cika alkawuran da ke rataye a wuyansu na tarihi don kawo karshen kawanyar da aka yi wa Gaza.
Kakakin kungiyar Houthi, Yahya Saree, a baya ya wallafa sako a shafinsa na soshiyal midiya da ke cewa za su hana jirage bi ta Bahar Maliya domin zuwa Isra'ila idan ba a bari an shigar da kaya irin su abinci da magunguna cikin Gaza ba.
Shugaban Houthi Abdulmalik al Houthi ya yi barazanar kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila da ke Bahar Maliya a wani jawabi da ya gabatar ta gidan talbijin ranar 14 ga watan Nuwamba.
2300 GMT — Isra'ila ta gode wa Amurka kan hawa kujerar-na-ki game da tsagaita wuta a Gaza
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gode wa Amurka kan hawa kujerar-na-ki game da kudurin dokar da ya nemi a tsagaita wuta nan-take a Gaza.
"Ina matukar godiya game da matakin gaskiya da Amurka ta dauka a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya," a cewar firaiministan Isra'ila a wani jawabi da ya gabatar ta gidan talbijin.
"Ya kamata sauran kasashe su fahimci cewa ba zai yiwa a goyi bayan kawar da Hamas da kuma kira-kiraye na kawar da Hamas a lokaci guda ba," in ji shi.
"Za mu ci gaba da fafutukar ganin an kawar da Hamas da hana ta cim ma maradunta.”