Sarkin Kuwait Nawaf al-Ahmad al-Sabah ya rasu

Al-Sabah ya rasu da safiyar Asabar bayan an kai shi asibiti sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

By Mustapha Kaita
Sarkin ya rasu yana da shekara 86 da haihuwa. / Hoto: AA / Others

Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah ya rasu a ranar Asabar da safe.

Ministan Harkokin Masarautar Kuwait Mohammad Abdullah Al-Mubarak Al-Sabah ya ce sarkin ya rasu yana da shekara 86 da haihuwa.

A cewarsa, an kai sarkin asibiti da safe sakamakon bukatar gaggawa amma daga baya Allah ya yi masa rasuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kuwait ya ruwaito.

Ya bayyana cewa ko a watan da ya gabata sai da aka kai sarkin asibiti sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sheikh Nawaf ya zama yarima mai jiran gado a 2006, bayan dan uwansa Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah ya nada shi.

Ya zama Sarkin Kuwait bayan rasuwar dan uwan nasa a Satumbar 2020 a lokacin da yake da shekara 91 da haihuwa.

A halin yanzu Sheikh Mishal al-Ahmad al-Sabah mai shekara 83 shi ne yarima mai jiran gado na kasar