| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben Kodin kusan 100,000
Hukumar ta ce ta kuma kama wata dattijuwa mai shekara 70 tare da danta da kilo 117.900 na wiwi.
NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben Kodin kusan 100,000
NDLEA na yawan kama masu safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya. / Hoto: NDLEA / Others

Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce ta yi kamen miyagun kwayoyi masu dumbin yawa daf da Bikin Kirisimeti.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa daga cikin miyagun kwayoyin da ta kama har da kwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben maganin tari mai dauke da kodin kusan 100,000.

Hukumar ta ce ta kama kwayoyin na Tramadol a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas tare da da hadin gwiwa da jami’an kwastam da sauran jami’an tsaro.

Hukumar ta ce an shigo da kwayoyin ne daga birnin Hamburg na Jamus. A cewar sanarwar, kwayoyin na cikin manyan kwalaye 100 wadanda baki dayansu nauyinsu ya kai kilo 7,150.

Haka kuma hukumar ta ce jami’anta da ke aiki a Legas sun kai wani samamen a wasu shaguna biyu a ranar Laraba 20 ga watan Disamba a kasuwar duniya da ke yankin Ojo.

NDLEA ta ce bayan sun yi bincike sai suka gano kwali 258 na maganin tari na ruwa mai dauke da kodin da kuma kwali takwas na kodin din amma na kwaya.

Kwalayen na dauke da kwalabe 49,200 na maganin tarin na ruwa sai kuma kwayoyi 46,200.

Hukumar ta ce washe gari jami’an hukumar sun kai samame a wani gida a unguwar Mushin ta ke jihar ta Legas inda suka kama wata dattijuwa mai shekara 70 mai suna Selifat Funke Cole da danta Babajide Ayorinde Cole inda aka kama su da kilo 117.900 na wiwi.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Putin ya ce Rasha ta fi Ƙasashen Yamma masu 'mulkin mallaka' zama abokiyar hulɗar gaskiya ga Afirka
Yadda nasarar Lula da Silva a zaɓen Brazil na 2026 za ta yya buɗe sabbin damarmaki ga Afirka
An kashe aƙalla Kiristoci ’yan Orthodox 60 a hare-hare a yankin Oromia na Ethiopia
Nijar ta zargi Chadi da haɗa baki da Faransa wajen kai mata hari
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje