| Hausa
DUNIYA
4 MINTI KARATU
Isra'ila za ta maye gurbin ma'aikata Falasdinawa sama da 80,000 da 'yan nahiyar Asia
Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 87 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 21,822 tare da jikkata 56,451 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira.
Isra'ila za ta maye gurbin ma'aikata Falasdinawa sama da 80,000 da 'yan nahiyar Asia
Isra'ilar ta ce za ta maye gurbin ma'aikatan da wasu 'yan kasashen nahiyar Asia. / Hoto: Reuters / Others

1540 GMT — Isra'ila za ta maye gurbin ma'aikata Falasdinawa sama da 80,000 da 'yan nahiyar Asia

Hukumomi a Isra’ila na shirin gabatar da wani kudiri wanda yake so a maye gurbin ma’aikatan kwadago Falasdinawa da na wasu kasashe a Isra’ila.

Kafar watsa labaran Isra’ila ta KAN a ranar Litinin ta ruwaito cewa ana son aiwatar da wannan shirin a 2024 domin rage dogaro da leburori Falasdinawa.

Ana sa ran gabatar da kudirin a gaban Majalisar Tattalin Arziki ta Isra’ila nan da makonni biyu.

A karkashin shirin, Isra’ilar na son kawo ma’aikata 80,000 daga kasashe wadanda suka hada da Sri Lanka da China da India da Thailand da Moldova.

0320 — Mayakan Al-Qassam Brigades sun harba rokoki birnin Tel Aviv da kewayensa

Mayakan Al-Qassam Brigades, wato bangaren soji na kungiyar Falasdinawa ta Hamas, sun harba manyan rokoki daga Zirin Gaza zuwa birnin Tel Aviv na Isra'ila da garuruwan da ke kewayensa da sanyin safiyar Litinin, abin da ya sa jiniya ta yi ta kuka.

Gidan rediyon Rundunar Sojin Isra'ila ya ce haka kuma an harba rokoki a biranen Rishon Lezion, Lod, Ramla, Bnei Brak da Sderot baya ga wani matsugunin Yahudawa mai suna Modi'in Illit da ke tsakiyar Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

A wani sako da suka wallafa a manhajar Telegram, mayakan Al-Qassam Brigades sun tabbatar da cewa sun harba bama-bamai a Tel Aviv da kewayensa.

"Al-Qassam Brigades na yin luguden wuta da makaman roka samfurin M90 a birnin Tel Aviv da kewayensa domin yin raddi ga kisan kiyashin da Yahudawa suke yi wa fararen-hula,” in ji sanarwar.

Kazalika sanarwar ta nuna bidiyoyin harin rokokin da kungiyar ta kai.

Babu bayani kan ko hare-haren sun yi sanadin mutuwa ko jikkatar wani ko wasu.

0000 GMT —Isra'ila za ta sallami wasu sojojinta na shirin ko-ta-kwana daga yakin Gaza

Rundunar sojin Isra'ila za ta sallami wasu daga cikin sojojinta na shirin ko-ta-kwana da ke yaki a Gaza, a wani mataki da ta ce zai taimaka wa tattalin arzikinta a yayin da kasar take shirin kaddamar da dogon yaki a yankin.

"Wasu daga sojojin shirin ko-ta-kwana za su koma wurin iyalansu da kuma bakin aikinsu a wannan makon," a cewar kakakin rundunar sojin Isra'ila Rear Admiral Daniel Hagari.

"Hakan zai bunkasa tattalin arziki, sannan ya ba su damar samun kuzari a jikinsu gabanin ayyukan da za su yi a wannan shekarar, kuma za mu ci gaba da yaki, kana za mu bukace su."

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji