| Hausa
DUNIYA
4 MINTI KARATU
Bulletproof Dreams: Turkiyya ta yi baje-kolin zane-zanen yaran Gaza
An yi baje-kolin ne domin jan hankulan duniya game da bala'i da mawuyacin halin da yaran Falasdinu ke ciki sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kai musu.
Bulletproof Dreams: Turkiyya ta yi baje-kolin zane-zanen yaran Gaza
Baje-kolin yana nuna irin tsananin da yara a Gaza suke ciki. An nuna irin halin da suke ciki ta hanyar zane-zane, in ji Emine Erdogan,  Mai Dakin Shugaban yayin da take zagayawa tare da Daraktan Sadarwa Fahrettin Altun domin ganin zane-zane./Hoto:OTHER / Others

Daraktan Sadarwan Turkiyya ya jan hankalin duniya game da mawuyacin halin da yaran Gaza ke ciki a yayin bude baje-kolin zane-zane da aka yi a kansu.

An bude baje-kolin mai suna "Bulletproof Dreams: Gaza Child Artists Exhibition" a Turancin Ingilishi a Dandalin Taksim da ke birnin Istanbul ranar Juma'a wanda ya samu halartar Mai Dakin Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan da Daraktan Sadarwa na kasar Fahrettin Altun.

"Dole mu zama muryar kananan yaran Falasdu wadanda (Isra'ila) ta kwace 'yancinsu na rayuwa," in ji mai dakin shugaban kasa, tana mai jaddada cewa Turkiyya za ta ci gaba da kokarin da take yi na kawo karshen cin zarafin da Isra'ila take yi wa Falasdinawa.

Shi ma Altun ya yi makamancin wannan jawabi sannan ya sha alwashin cewa Turkiyya ba za ta taba karaya ba wajen fadin gaskiya, kuma ba za ta daina kare hakkin kananan yara da ake kashewa ba.

"Muguntar Isra'ila ba ta da hallacci kowanne iri...Wannan ya nuna cewa babu shakka Isra'ila tana nufar kananan yara ne da makomar Falasdinu a yakin da take yi, inda take aikata laifukan yaki da kuma yin kisan kare-dangi," a cewar daraktan sadarwar.

Nuna yaki da barna

Dan jarida Abdullah Aytekin ne ya tattara zane-zanen da aka yi baje-kolinsu, wadanda suka kai guda 266, da yaran Gaza, ciki har da wadanda Isra'ila ta kashe, suka yi.

Mona, 'yar shekara 6 daga Gaza wadda ta ga lokacin da Isra'ila ta kashe mahaifiyarta a Yakin Gaza na 2008-09 da kuma kisan 'yan uwanta 26, na cikin wadanda suka yi zane-zanen.

Zane-zanen, "Bulletproof Dreams: Gaza Child Artists Exhibition", mai fadin sikwaya mita1350, an yi su ne domin jan hankalin duniya game da bala'in da yaran Gaza ke ciki sakamakon hare-haren Isra'ila.

Kazalika akwai bangaren da aka yi baje-kolin zane-zane na 'yan jarida da likitoci da suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kaddamar tun ranar 7 ga watan Oktoba bayan Hamas ta kai mata harin ba-zata.

Tun daga wancan lokacin, Isra'ila ta kashe Falasdiawa akalla 21,110, galibinsu mata da kananan yara, sannan ta jikkata 55,243, a cewar hukumomi.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji