| Hausa
DUNIYA
6 MINTI KARATU
Isra’ila ta kashe mataimakin shugaban Hamas Saleh Arouri
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 88 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 21,978 da jikkata 56,697a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira.
Isra’ila ta kashe mataimakin shugaban Hamas Saleh Arouri
Arouri shi ne mamba na Hamas mafi girma da Isra'ila ta kashe tun bayan soma wannan yaki. / Hoto: Others / Others

1822 GMT— Isra’ila ta kashe mataimakin shugaban Hamas Saleh Arouri

Wani jirgi maras matuki na Isra’ila ya kai hari a wani ofishin kungiyar Hamas a wajen birnin Beirut na Lebanon inda ya kashe mutum hudu.

Daga cikin wadanda harin ya kashe har da mataimakin shugaban Hamas Saleh Arouri, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya tabbatar.

Wani babban jami’in tsaro a Beirut ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kashe Arouri tare da jami’an tsaronsa.

Arouri shi ne mamba na Hamas mafi girma da Isra'ila ta kashe tun bayan soma wannan yaki a ranar 7 ga watan Oktoba.

1314 GMT — Isra'ila ta kashe mutane da dama a sabbin hare-haren da ta kai Khan Younis — PRC

Kungiyar bayar da agaji ta Palestinian Red Crescent ta ce dakarun Isra'ila sun kashe mutane da "dama" tare da jikkata wasu a sabbin hare-haren da ta kai a hedkwatarta da ke birnin Khan Younis na Gaza.

Jiragen yakin Isra'ila sun yi luguden wuta a hawa na takwas na ginin kungiyar ta Palestinian Red Crescent lamarin da ya haddasa mutuwar mutane da yawa, a cewar kungiyar.

0901 GMT — Isra'ila za ta kare kanta a Kotun ICJ kan kisan kare-dangi a yankin Falasdinu

Shugaban Majalisar Tsaron Isra'ila, Tzachi Hanegbi, ya ce kasarsa ba za ta ki halartar karar da Afirka ta Kudu ta shigar a kanta ba a Kotun Hukunta Manyan Laifuka (ICJ) bisa kisan Falasdinawa fiye da 21,000, galibinsu mata da kananan yara a Gaza da ta mamaye ba.

Da yake magana da jaridar Yediot Ahronot, Hanegbi ya bayyana cewa Isra'ila za ta shiga cikin shari'ar a matsayin na wacce ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Hana Kisan Kara-Dangi.

Ya musanta cewa sun aikata kisan kara-dangi a Gaza, yana mai cewa zargin "karya" ce .

"A matsayin Isra'ila na wacce ta dade da sa hannu a yarjejeniyar hana kisan kare-dangi, ba za ta ki halartar shari'a kan batun ba. Za mu halarci zaman shari'ar kuma za mu karyata zargin da ake yi mana na zubar da jini," in ji Hanegbi.

2335 GMT —Hamas ta nemi ICRC ta dauki mataki kan dokokin da Isra'ila ta karya na kare 'yancin Falasdinawa fursunoni

Kungiyar Hamas da ke fafutukar kare mutuncin Falasdinawa ta yi kira ga kungiyar agaji ta International Committee of the Red Cross [ICRC] da ta tattara irin dokokin kara hakkin dan'adam na Falasdinawan da ke tsare a gidajen yari da Isra'ila ta karya, musamman yadda take gallaza wa mata.

A wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta bukaci ICRC da sauran kungiyoyin kare hakkin dan'adam "su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na daukar mataki kan cin zali da take 'yanci da Isra'ila ke yi wa mata Falasdinawa wadanda ke tsare a gidajen yarinta."

Sanarwar ta kara da cewsa "Matan Falasdinawa da ke tsare a gidajen yari suna fuskantar tsananin rashin abinci da hana su magunguna."

Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa Falasdinawa sama da 7,800 ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila, ciki har da mata 80.

2140 GMT —Kotun Kolin Isra'ila ta yi watsi da shirin Netanyahu na rage ikon alkalai

Kotun Kolin Isra'ila ta yi watsi da wani muhimmin bangare na shirin Firaiminista Benjamin Netanyahu na yin garambawul da zai rage karfin iko ga fannin shari'a na kasar.

Alkalai takwas ne suka yi watsi da kudirin yayin da bakwai suka goyi bayansa.

Kudurin, wanda Majalisar Dokokin kasar ta amince da shi a watan Yulin da ya gabata, ya soke ikon da Kotun Koli take da shi na ayyana matakan da gwamnati ta dauka a matsayin marasa kan gado sannan ya rage karfin ikon alkalai.

Majalisar Dokokin Isra'ila mai suna Knesset ta yi kudirin kwaskwarima ranar 24 ga watan Yuli, sannan ta amince da shi.

Sai dai gamayyar jam'iyyun da ke mulkin kasar ta yi fatali da hukuncin na ranar Litinin, inda Ministan Shari'a Yariv Levin ya ce hakan nuna kyama ne ga "hadin kai" da ake bukata a lokacin yaki.

Jam'iyyun hamayya a kasar sun goyi bayan hukuncin, inda shugaban jam'iyyar adawa Yair Lapid ya ce yana mara wa kotun cikakken baya "a rawar da take takawa wajen kare al'ummar Isra'ila."

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda