Dan bindiga ya harbe limamin wani masallaci a Amurka

An harbi Imam Hassan Sharif fiye da sau daya bayan sallar asubahi a wajen Masallacin Masjid-Muhammad-Newark, a cewar hukumomi, a yayin da ake samun karuwar kin jinin Musulmai a Amurka tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza.

By Nasidi Adamu Yahaya
An harbi Imam Hassan Sharif fiye da sau daya bayan sallar asubahi a wajen Masallacin Masjid-Muhammad-Newark, a cewar hukumomi. / Hoto: Masjid-Muhammad-Newark / Others

Limamin nan da wani dan bindiga ya harba a wajen masallacin Newark a jihar New Jersey ya mutu sakamakon raunukan da ya ji, a cewar hukumomi a Amurka.

Ranar Laraba Antoni Janar na New Jersey Matt Platkin ya ce kisan Imam Hassan Sharif ya girgiza al'ummar jihar baki daya, inda ya kara da cewa babu wata hujja da ke nuna cewa an kai masa hari ne saboda kyamar Musulunci.

Limamin yana cikin motarsa lokacin da maharbin ya harbe shi fiye da sau daya a kusa da masallacin, a cewar Mai Shigar da Kara na Yankin Essex Ted Stephens a taron manema labarai.

Jami'an tsaro sun soma farautar maharin, sannan gwamnan jihar ya yi alkawarin tabbatar da tsaro a wuraren ibada.

An harbi Imam Hassan Sharif fiye da sau daya bayan sallar asubahi a wajen Masallacin Masjid-Muhammad-Newark, a cewar Daraktan Samar Da Tsaro na Newark Fritz Frage.

An garzaya da shi wani asibiti cikin mawuyacin hali, sai dai ya mutu sakamakon raunukan da aka ji masa da bindiga, a cewar hukumomi.

Frage ya ce ana gudanar da bincike a kan harbin, kuma babu wani karin bayani.