1346 GMT — Rasha ta nemi Hamas ta saki mutanen da take garkuwa da su
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Rasha Mikhail Bogdanov ya gana da mamban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Musa Abu Marzouk a birnin Moscow babban birnin kasar, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha ta sanar.
Kasar Rasha ta bukaci kungiyar Hamas da ta sako dukkan mutanen da ta yi garkuwa da su a tattaunawar da ta yi da kungiyar Falasdinu a birnin Moscow, tana mai cewa halin da ake ciki na bala'in jinƙai a Gaza ya kai ƙololuwa.
Jami'in diflomasiyyar Rasha Mikhail Bogdanov "ya jaddada bukatar gaggauta sakin fararen hula da aka kama a harin na ranar 7 ga watan Oktoba" a tattaunawar da ya yi da dan siyasan Hamas Musa Abu Marzouk, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha.
1230 GMT — Jarirai kusan 20,000 aka haifa a Gaza tun fara yakin isra'ila a yankin
Jarirai kusan 20,000 aka haifa ana cikin yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, yayin da yara 135,000 ke fuskantar "mummunan haɗarin kamuwa da tamowa" a Gaza, a cewar UNICEF a ranar Juma'a.
Mai magana da yawun UNICEF Tess Ingram ya kuma ce adadin ya yi daidai da jariri daya da ake haifa kusan kowane minti 10 tun daga ranar 7 ga Oktoba, lokacin da rikicin ya fara.
Ya shaida wa manema labarai a Geneva cewa: "Halin da mata masu juna biyu da jarirai ke ciki a Zirin Gaza ya wuce gona da iri, kuma yana buƙatar gabatar da ayyuka na gaggawa."
"Halin ha'u'la'in da yara da mata ke ciki har yake sanadin mutuwarsu ya sake ta'azzara, sakamakon rushewar da tsarin kiwon lafiyar ke ciki," Ingram ya jaddada, yana mai cewa uwaye na fuskantar wasu irin ƙalubale masu ta da hankali ta wajen kula da lafiyarsu, da abincin da za su ci musamman a lokacin ciki da goyo.
1108 GMT — Yawan mutanen da aka kashe a hare-haren Isra'ila a Gaza ya ka
The health ministry in Gaza has said Israel's bombardment has killed 24,762 people in the besieged Palestinian territory.
Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce harin bam da Isra'ila ta kai ya kashe mutum 24,762 a yankin Falasdinawa da aka yi wa kawanya.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce adadin ya hada da mutum 142 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, yayin da mutum 62,108 suka samu raunuka tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ba kakkautawa a ranar 7 ga watan Oktoba bayan harin Hamas.














