| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Har yanzu ba mu samu labarin fitar Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinmu ba - ECOWAS
Kungiyar ECOWAS ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba.
Har yanzu ba mu samu labarin fitar Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinmu ba - ECOWAS
ECOWAS ta kara da cewa tana "aiki babu kakkautawa da wadannan kasashe domin ganin an dawo da tsarin mulki."/Hoto:Fadar shugaban Nijeriya / Others

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba.

A ranar Lahadi da hantsi kasashen uku suka fitar da sanarwa cewa sun fice daga kungiyar saboda ta gaza taimaka musu wurin shawo kan rashin tsaron da ke addabasu da ma sauran kalubalen da suke fama da su.

"Har yanzu Hukumar ECOWAS ba ta samu bayani a hukumance daga kasashen uku ba da ke nuna cewa sun fita daga cikinta," a cewar wata sanarwa da ECOWAS ta wallafa a shafinta na X.

Kungiyar ta ce ta yi mamakin "wannan mataki."

ECOWAS ta kara da cewa tana "aiki babu kakkautawa da wadannan kasashe domin ganin an dawo da tsarin mulki."

"Burkina Faso, Nijar, da Mali mambobinmu ne masu matukar muhimmanci kuma hukumar nan za ta yi bakin kokarinta wurin samar da mafita ga rikicin siyasar da suke ciki."

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai