Majalisar Dattawan Nijeriya ta nemi a ɗauki ƙarin sojoji 100,000 don magance rashin tsaro

Gidan talabijin ɗin ƙasar (NTA) ya ruwaito cewa majalisar ta kuma kafa wani kwamiti na wucen gadi domin yin bincike kan ware kuɗi da kashe kuɗi da kuma sakamakon shirin kare makarantu.

By
Sojojin Nijeriya suna ƙoƙarin daƙile matsalar rashin tsaro da ƙsar ke fama da shi

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi kira ga rundunar sojin ƙasar da ta ɗauki ƙarin sojoji 100,000 domin magance matsalar rashin tsaro a sassan ƙasar.

Gidan talabijin ɗin ƙasar (NTA) ya rawaito cewa majalisar ta kuma kafa wani kwamiti na wucin gadi domin yin bincike kan ware kuɗi da kashe kuɗi da kuma sakamakon shirin kare makarantu.

Majalisar ta amince da waɗannan ƙudurorin ne bayan wani majalisar uya tafka muhawara kan sace ɗalibai mata 25 da wasu ‘yan bindiga suka a makarantar ‘yan mata ta gwamnati ta Maga, a jihar Kebbi.

Majalisar ta yi kakkausar suka kan aika-aikar, inda ta jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Kazalika Majalisar ta yi alhinin rasuwar Birgediya Janar Uba da saurna sojojin da aka kashe a jihar Borno.

Nijeriya tana fuskantar matsalolin rashin tsaro a sassan ƙasar, lamarin da ya sa dubban mutane suka rasa rayukansu tare da raba da yawa da muhallansu.