| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Zanga-zanga ta ɓarke a Senegal bayan sanar da ɗage zabe
A ranar Asabar ne shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya sanar da ɗage zaɓen ƙasar har sai baba ta gani.
Zanga-zanga ta ɓarke a Senegal bayan sanar da ɗage zabe
Masu zanga-zangar sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da ɗage zaɓen. Hoto AFP / Others

Jami'an tsaron Senegal sun tarwatsa dandazon jama'a da suka taru a Dakar babban birnin ƙasar ranar Lahadi domin nuna adawa da ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka yi, wanda a da za a yi shi ne a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Shugaba Macky Sall ya sanar a ranar Asabar da ta gabata cewa za a jinkirta kaɗa ƙuri'ar zuwa ranar da ba a bayyana ba saboda taƙaddama kan jerin sunayen ƴan takara - matakin da jam'iyyun adawa suka yi watsi da shi.

Kimanin masu zanga-zanga 200 ne suka hana zirga-zirgar ababen hawa a babban titin birnin Dakar tare da saka shingayen na ƙonannun tayoyi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

'An kama tsohuwar Firaiminista'

An kama tsohuwar Firaiministar Senegal Aminata Toure, wadda a yanzu ita ce babbar 'yar gaba-gaba a zanga-zangar nuna adawa da ɗage zaɓen shugaban ƙasa, kamar yadda ɗan majalisar jam'iyyar adawa Guy Marius Sagna ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

"Na tabbatar da cewa 'yan Jandarma sun kama Aminata Toure," in ji shi. Shugaban ƙasar Macky Sall ne ya naɗa Toure firaiminista amma daga baya ta koma jam'iyyar adawa.

Ɗaruruwan magoya baya na adawa da ke zanga-zangar sun koma kan gefen titunan bayan ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun harba hayaƙi mai sa hawaye. Har yanzu dai hukumomin ƙasar ba su ce komai ba kan sabon lamarin.

Senegal dai ba ta taɓa jinkirta zaɓen shugaban ƙasa ba kuma akwai rashin tabbas kan abin da zai biyo baya.

ECOWAS ta bukaci a kwantar da hankula

A bara, ƙasar ta fuskanci mummunar zanga-zanga bayan da aka ɗaure jagoran ƴan adawa Ousmane Sonko, inda magoya bayansa suka ce wata dabara ce ta hana shi tsayawa takara a zaɓen.

Shekaru da dama ana kallon Senegal a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen Yammacin Afirka mafi kwanciyar hankali a tsarin dimokuraɗiyya, amma rashin ci-gaban siyasa a ƙasar ya haifar da damuwa.

Bayan sanarwar da Sall ya yi ta kafar talabijin, ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta nuna damuwa game da yanayin da ya kai ga ɗage zaben, tare da yin kira da a sanya sabuwar ranar zaɓe cikin gaggawa. An kuma buƙaci a kwantar da hankula da bin matakin sasantawa.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Afirka ta sami tallafin $900m domin faɗaɗa fasahar girki na zamani mara gurɓata muhalli
Rasha na son ƙarfafa alaƙa da Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) - Lavrov
Sojojin Sudan sun ƙwace ƙauyen Al-Kurmuk bayan arangama da dakarun RSF
Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu sun kama masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba fiye da 200
Ƙawancen tsaro na Turkiyya da Afirka na haɓaka a tsarin duniya da ke sauyawa
Jami’an leken asiri sun lalata yunƙurin ‘yan ta’addan Daesh na kai hari a garuruwan Morroco bakwai
'Yansandan Afirka Ta Kudu sun ce mutuwar ɗan Nijeriya ba ta da alaƙa da tashin hankalin ci-rani
MDD ta yi gargaɗin cewa hare-haren RSF na iya mayar da birnin Al-Obeid na Sudan kamar Al-Fasher
Rikicin diflomasiyya ya kaure tsakanin Ghana da Afirka ta Kudu kan mutuwar ɗan Ghana
Burkina Faso, Mali da Nijar sun gabatar da sanarwar ficewa daga ICC, in ji kotun
Sojojin Mali sun raka motocin dakon mai da abinci 940 zuwa Bamako saboda fargabar harin ta'addanci
Sojojin Burkina Faso sun ce sun kashe 'yanta'adda fiye da 400 a wani hari da suka daƙile
An gurfanar da ɗalibai mata takwas a kotu a Kenya kan zargin kisan abokan karatunsu a gobara
Yadda Nijeriya ke fama da hauhawar farashin gas din girki
MDD ta yi gargaɗin cewa cutar Ebola na iya jefa kusan mutane miliyan 1 cikin talauci a DRC
Afirka ta Kudu ta mai da fiye da mutum 25000 kasashensu kafin wa'adin 30 ga Yuni na masu ƙyamar baƙi
Yadda abinci ke yin kisan mummuƙe a Afirka
Burkina Faso ta kawo ƙarshen dangantakar diflomasiyya da Faransa
Fiye da mutum 1,400 sun tsere daga jihar North Darfur ta Sudan a yini ɗaya yayin da ake zafafa yaƙi
Nijeriya da ƙasashe 4 sun ƙaddamar da sabuwar hukuma kan hanyar Abidjan zuwa Lagos ta $16bn