AFIRKA
3 MINTI KARATU
AFCON 2023: Tinubu ya jinjina wa ƴan wasan Super Eagles
"Shugaba Tinubu yana jinjina ga Super Eagles da masu horarwa da dukkan masu gudanarwa na tawagar bisa jajircewarsu da sadaukarwa har suka kawo wannan mataki na gasar," in ji sanawar.
AFCON 2023: Tinubu ya jinjina wa ƴan wasan Super Eagles
Shugaba Tinubu ya ce ya lura da ƙalubalen da  ƴan wasan Super Eagles suka fuskanta kafin su kai matakin ƙarshe na gasar ta AFCON 2023. /Hoto:  Super Eagles/X
12 Fabrairu 2024

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya jinjina wa tawagar ƙwallon ƙafar, Super Eagles, bisa bajintar da ta nuna a gasar cin kofin nahiyar Afirka duk da yake ba ta ɗauki kofin ba.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar ranar Lahadi jim kaɗan bayan kammala gasar cin kofin Afirka, wadda ƙasar Côte d’Ivoire ta lashe bayan ta doke Nijeriya da ci 2-1.

"Shugaba Tinubu yana jinjina ga tawagar da masu horarwa da dukkan masu gudanarwa na tawagar bisa jajircewarsu da sadaukarwa har suka kawo wannan mataki na gasar," in ji sanawar.

Ya ce ya lura da ƙalubalen da suka fuskanta kafin su kai matakin ƙarshe na gasar ta AFCON 2023.

"Bai kamata wannan lamari mai wucewa ya kashe mana karsashi ba, ya dace ya haɗa kawunanmu domin mu yi aiki tuƙuru. Mu, babbar ƙasa ce da tutar kore-fari-kore ta haɗa mu, abin da ke nufin jajircewa da farin-ciki da fata na gari da aiki tuƙuru da ƙaunar juna," a cewar Shugaba Tinubu.

Ƙasar Côte d’Ivoire ce dai ta yi nasarar ɗaukar kofin nahiyar Afirka bayan ta doke Nijeriya da ci 2-1 a wasan da suka fafata a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan, babban birnin ƙasar.

Tawagar Super Eagles ce ta soma cin ƙwallo ta hannun William Troost-Ekong gabanin a tafi hutun rabin lokaci inda ya doka ƙwallon da ka a ragar the Elephants.

Sai dai ɗan wasan Côte d’Ivoire Franck Kessie ya farke ƙwallon jim kaɗan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Daga nan ne fa ƴan wasan Côte d’Ivoire suka matsa wajen kai hari a gidan Nijeriya har lokacin da Sebastien Haller ya zura ƙwallo a ragar Super Eagles saura minti tara a kammala wasa.

Wannan ne karo na uku da Côte d'Ivoire ta ɗauki kofin nahiyar Afirka.

Côte d'Ivoire ta soma gasar da ƙafar-hagu inda ta sha kashi sau biyu a matakin rukuni, ciki har da wulaƙancin da Equatorial Guinea ta yi mata a ci 4-0. Amma daga bisani tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar ta zage dantse har ta kai wannan mataki.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta
Paul Biya na Kamaru: Shugaban da ya fi tsufa a duniya ya sha rantsuwar kama aiki karo na takwas
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata
Sabbin hotunan tauraron dan'adam sun gano alamun 'kaburburan bai-daya a El-Fasher a Sudan
MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu
Trump ya ce bai kamata Afirka ta Kudu ta kasance cikin G20 ba, ba zai je taronta a Johannesburg ba
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
An kashe mutane 40 a harin da aka kai wa taron jana'iza a yankin Kordofan na Sudan: MDD
Yadda biranen Afirka mafiya tsafta suke bayyana sauyin da ake samu a nahiyar
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Harin jirgin sama maras matuƙi na RSF ya kashe mutane da dama a lardin Kordofan na Arewa a Sudan
Fiye da mutum 1,500 sun rasa matsugunansu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro: MDD
Dakarun RSF sun kashe mata 300, sun yi wa 25 fyaɗe cikin awa 48 a Al Fasher – Minista
Amurka ta buƙaci a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin Sudan, ba amfani da ƙarfin soja ba
Ana fargabar dubban mutane na cikin 'mummunan hatsari' a birnin Al Fasher na Sudan da RSF ta ƙwace
Shugabar Tanzania Samia Hassan ta lashe zaɓen ƙasar da kashi 97.66 cikin 100
Tchiroma Bakary: Sojojin Kamaru sun yi wa jagoran 'yan adawar kasar rakiya zuwa wuri mai 'aminci'
Kudirin 1325 ya cika shekara 25: Me ya sa dole Afirka ta jagoranci samar da zaman lafiya a duniya
Dubban mutane sun tsere daga North Kordofan yayin da RSF ta zafafa kai hari a yankin Darfur na Sudan
Fararen-hula 177,000 sun maƙale a Al Fasher na Sudan, yayin da RSF ke ci gaba da kisa - Likitoci