| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Gwamnatin Kano za ta soma biyan albashi a tsarin IPPIS
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da manhajar daukar bayanan ma’aikatan gwamnati da ƴan fansho da ƴan siyasa wajen biyansu albashi a tsarin nan na IPPIS.
Gwamnatin Kano za ta soma biyan albashi a tsarin IPPIS
Abba Gida-Gida ya zamo mutum na farko da aka dauki bayanansa aka dora a kan manhajar tsarin. / Others

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da manhajar daukar bayanan ma’aikatan gwamnati da ƴan fansho da ƴan siyasa wajen biyansu albashi a tsarin nan na IPPIS.

Tsarin IPPIS tsari ne da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta daɗe tana amfani da shi wajen biyan ma’aikatanta, inda ake ɗaukar bayansu ciki har da zanen yatsun hannu, da nufin rage rashin gaskiya da wasu ke yi na yin aiki a hukumomin gwamnati daban-daban suna karɓar albashi fiye da ɗaya.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Talata, Gwamna Abba Gida-Gida kamar yadda aka fi saninsa, ya ce ya bijiro da wannan tsari ne don tabbatar da gaskiya da rashin rufa-rufa da ƙeƙe-da-ƙeƙe wajen tafiyar da al'amuran gwamnati.

Gwamnan ya ƙaddamar da tsarin da aka bai wa suna Kano Integrated Personal and Payroll Information System (KIPPIS) ne a wajen taron Majalisar Zartarwa karo na 12 da aka yi a fadar gwamnatin jihar.

Abba Gida-Gida wanda ya zamo mutum na farko da aka dauki bayanansa aka dora a kan manhajar tsarin, ya ce za a yi amfani da shi ne a duka matakin jiha da na ƙananan hukumomi "don bin tsarin sha'anin kuɗi da duniya ke kai a yanzu."

Gwamnan ya nei mambobin kwamitin ƙaddamar da tsarin KIPPIS da su tabbatar da cewa sun ɗauki bayanan dukkan ma'aikatan gwamnati da ƴan fanshi da masu riƙe da muƙaman siyasa don samun nasarar tsari a faɗin jihar.

Kazalika Babban Akawun jihar Alhaji Abdulkadir Abdussalam, ya ce za a tabatar da cewa ba a samun matsaloli ba a wajen bin tsarin KIPPIS ta kowane fanni da suka haɗa da rage kuɗaɗen mutane.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Mutane uku sun mutu bayan motar fasinja ta yi karo da giwa a gandun dajin Uganda
Shugaban Senegal Faye ya naɗa sabon firaminista da zai maye gurbin Sonko
Adadin mutanen da Ebola ta kashe a Jamuhuriyar Kongo ya wuce 200
Shugaban Senegal Faye ya sallami Firaministansa Ousmane Sonko
Kenya za ta rage farashin man dizel bayan zanga-zangar da aka yi kan tsadar makamashi
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar za ta ƙayyade kuɗin gidajen haya
Sierra Leone ta amince ta karɓi kashin farko na waɗanda aka taso ƙeyarsu daga Amurka
'Makashin Al Fasher' ya koma fagen daga a yaƙin Sudan: Rahoto
Nijar da China sun cim ma yarjejeniyar mai bayan watanni ana takaddama
Adadin mutanen da suka mutu a Congo saboda kamuwa da Ebola ya kai 131
Kenya ta kama wata mata bisa zargin damfarar Ba’amurke dala 431,000 a yarjejeniyar cinikin zinare
Dole Afirka ta daina bin umarnin manyan ƙasashen duniya
WHO ta bayyana ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Kongo a matsayin 'matsalar lafiya ta gaggawa'
Mutum 80 sun rasu a sabuwar ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Congo
Sojojin Sudan sun ƙwace iko da wani muhimmin birni a kusa da iyakar Habasha bayan arangama da RSF
Yakin Sudan: Yara na daga gomman da aka kashe a arangamar makonni biyu a Kordofan
Nijar na son ƙara adadin jihohinta daga 8 zuwa 19 da kuma sauya sunayen wasu jihohim
Shirin 'Big Catch-Up': Kokarin da ya kawo alluran rigakafi miliyan 100 ga yaran Afirka da aka manta
Ghana za ta kwashe ɗaruruwan 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu bayan hare-haren ƙin jinin baƙi
Bankin Ci-gaban Afirka ya amince da fitar da dala miliyan 61 don tallafa wa mata a Nijeriya