Gwamnatin Jihar Filaton Nijeriya ta saka dokar hana fita ta sa'o'i 48 a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa
Wata sanarwa da Kwamishiniyar Watsa Labaran Jihar, Joyce Lohya Ramnap, ta fitar ranar Lahadi tabbatar da cewa harin da aka kai Angwan Rukuba ya yi sanadiyar rasa rayuka da tare da jikkata wasu mutane.
Gwamnatin jihar Filato a arewa maso tsakiyar Nijeriya ta saka dokar hana fita a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa ta sa’o’i 48 bayan wani harin ‘yanbindiga da aka kai Gari Ya Waye a Angwan Rukuba ranar Lahadi da daddare.
Wata sanarwa da Kwamishiniyar Watsa Labaran Jihar, Joyce Lohya Ramnap, ta fitar ranar Lahadi tabbatar da cewa harin da aka kai Angwan Rukuba ya yi sanadiyar rasa rayuka da tare da jikkata wasu mutane.
Rahotanni dai sun ce lamarin ya auku ne ranar Lahadi da daddare lokacin da wasu ‘yanbindiga da ba a sani ba suka buɗe wuta kan mutane a Angwan Rukuba lamarin da ya kashe mutane 12 yayin da ya jikkata gommai.
“Gwamnatin jihar Filato tare da hukumomin tsaro na son su shaida wa mutane cewa an ƙaƙaba dokar hana fita ta sa’o’i 48 a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa nan-take daga ƙarfe 12 na dare na ranar 29 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Afrilu ta shekarar 2026,” in ji sanarwar.
“Gwamnatin a ƙarƙashin shugabancin mai girma, Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ta yi Allah wadai da wannan aikin dabbanci da aka yi babu gaira babu dalili kan waɗanda ba su ji ba basu gani ba kuma tana tabbatar wa mutane cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kama waɗanda suka aikata aika-aikar ta kuma gurfanar da su a gaban kuliya,” in ji Kwamishiniyar.
Ta ƙara da cewa “ Ana kira ga ‘yan jihar su kwantar da hankulansu, su mayar da hankali su kuma ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro ta hanyar ba su duk wasu bayanai da za su iya taimaka wa binciken da ake yi.”
Jihar Filato dai ta daɗe tana fama da rikici da ke da nasaba da ƙabilanci da addini da kuma rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Sai dai kuma kawo yanzu dai ba a tabbatar da cewa wannan harin na baya bayan nan yana da nasaba da irin hare-haren da aka saba gani a jihar ba ko kuma yana da nasaba ne da ‘yan ƙungiyar asiri kamar yadda wasu rahotanni ke cewa.