| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Dakarun Nijar sun daƙile harin ta’addanci kan filin jirgin sama na Tahoua
'Yanbindiga a kan babura sun kai hari filin jirgin sama na Tahoua, sai dai jami'an tsaro sun daƙile su ta hanyar musayar wuta inda suka kashe wasu daga cikin 'yanbindigan da kama biyar.
Dakarun Nijar sun daƙile harin ta’addanci kan filin jirgin sama na Tahoua
Jami’an tsaron na Nijar sun samu nasarar kashe wasu daga cikin maharan tare da kama biyar. / Others

Gwamnan Yankin Tahoua a Jamhuriyar Nijar, Souleymane Amadou Moussa, ya kai ziyara a ranar Litinin zuwa Sansanin Sojin Sama na 401 da ke Filin Jirgin Sama na Tahoua, bayan wani hari da wasu ’yanbindiga suka kai da daddare wanda dakarun tsaro suka samu nasarar daƙilewa.

Gwamnan, tare da rakiyar shugabannin hukumomin tsaro na yankin da kuma mambobin Kwamitin Tuntuɓa na Sabunta Tsarin Mulki, sun yi kewaye sansanin domin duba irin ɓarnar da aka yi tare da yaba wa jami’an tsaro kan saurin mayar da martani.

Harin ya faru ne da misalin karfe 3:05 na asuba agogon yankin, lokacin da wasu ’yanbindiga da suka iso kan babura suka yi yunkurin kai farmaki kan filin jirgin. A cewar jami’ai, maharan sun samu damar lalata wasu garejin ajiye jirage marasa matuƙa kafin jami’an tsaro su fatattake su.

Masu AlakaTRT Afrika - An ji harbe-harbe da ƙarar fashewar wasu abubuwa a yankin Tahoua na Nijar

Hukumomi sun ce a yayin artabun, dakarun ƙasar kaɗan sun samu raunuka, yayin da aka kashe wasu daga cikin maharan. Haka kuma an kama mutane biyar da ake zargi, da taimakon mazauna yankin. Jami’an tsaro sun ce an kwato kuɗi masu yawa da wasu kayayyaki daga hannun waɗanda ake zargin.

A yayin ziyarar, gwamnan da tawagarsa sun duba wuraren da harin ya shafa a filin jirgin, ciki har da wuraren aiki na jami’an tsaro da shingen tsaron da maharan suka yi ƙoƙarin kutsawa.

Daga nan tawagar ta wuce zuwa Hedikwatar Rundunar ’YanSanda ta Yanki (DRPN), inda ake tsare da mutanen biyar da aka kama.

Da yake magana bayan ziyarar, Gwamna Moussa ya ce manufar ziyarar ita ce duba halin da ake ciki bayan harin. Ya tabbatar da cewa duk da cewa wasu kayayyaki an lalata su amma ba sosai ba, martanin da dakarun tsaron suka mayar ya tilasta wa maharan janyewa cikin gaggawa.

Ya ce jami’an tsaron sun samu nasarar kashe wasu daga cikin maharan tare da kama biyar.

A madadin hukumomin ƙasar, gwamnan ya taya dakarun tsaron murna kan ƙwarewarsu da kuma saurin ɗaukar mataki.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar ƙasar da na duniya cewa an shawo kan lamuran a halin yanzu. A cewarsa, rayuwa a Tahoua na tafiya kamar yadda aka saba, filin jirgin sama na ci gaba da aiki cikin tsaro, kuma duk ayyukan filin jirgin suna gudana ba tare da tangarɗa ba.

Gwamna Moussa ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kasance cikin shiri da kula tare da taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar sanar da su duk wani abu da ya zama abin zargi.

Ya tunatar da jama’a cewa akwai lambobin waya kyauta da za su iya kira domin sanar da duk wata barazana, ta yadda jami’an tsaro za su iya daukar mataki cikin gaggawa.

Hukumomi sun tabbatar da cewa an kaddamar da bincike kan wannan lamari, yayin da ayyukan tsaro ke ci gaba a yankin.

Rumbun Labarai
An kashe mutum 10 tare da kama 11 a harin 'yanbindiga kan ayarin sojin Ghana
Ministan Tsaron Mali Camara ya yi musayar wuta da 'yanta'adda kafin a kashe shi
An kashe Ministan Tsaron Mali a harin ta'addanci: Al Jazeera
Turkiyya ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addanci da aka kai a kasar Mali
WHO ta amince da maganin maleriya na jarirai na farko
An bayar da rahoton fashewar bama-bamai da ƙarar bindigogi a kusa da barikin sojin Mali mafi girma
Dangote ya sha alwashin gina matatar mai a Gabashin Afirka tare da goyon bayan shugabanni
Aƙalla mutane 518 ne suka mutu a zanga-zangar bayan zaɓe a Tanzania: Bincike
Makomar abinci a Afirka: Bankin Duniya na fuskantar matsin lamba don ba wa ƙananan manoma fifiko
Nijar ta kori ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, NGO kusan 3,000 a kokarin ‘tsaftace ayyukansu’
China ta 'gode wa' ƙasashen Afirka da suka ƙi amincewa jirgin shugaban Taiwan ya wuce ta samaniyarsu
Yadda Ghana ke samun nasarar ɗaɓɓaka Kishin Afirka
Me Faransa ke nema a Kenya bayan korar ta daga Sahel?
Morocco ta saki magoya bayan Senegal da aka ɗaure kan hargitsin wasan ƙarshe na AFCON
Ziyarar Afirka: Fiye da mutum 500,000 ake sa ran sun halarci taron ibada na Fafaroma Leo a Kamaru
Yara mata ne suka fi cutuwa daga yaƙin Sudan da aka manta da shi
Fafaroma Leo ya nufi Kamaru ƙasa ta biyu a ziyararsa ta Afirka
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
Yadda yakin Iran ke shafar tattalin arziki, yanki da siyasar Afirka
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i