Trump: Za a kai wa tashoshin lantarki da gadojin Iran hari idan ba a buɗe mashigar Hormuz ba
Trump ya kuma ce Amurka ta ceto wani memban ma'aikatan jirgin F-15 “wanda ya ji rauni sosai kuma jarumi" daga "surƙuƙin tsaunukan Iran."
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazana a cikin wani rubutu cike da zage-zage a dandalin sada zumunta a ranar Lahadi, cewa zai kai hari kan tashoshin samar da wutar lantarki da gadajoji a Iran idan ba a buɗe Mashigar Hormuz ba washegari.
Bayan wa'adin awanni 48 da ya bayar a ranar Asabar, Trump ya rubuta a shafinsa na Truth Social cewa "Talata za ta kasance Ranar Tashoshin Wuta, da Ranar Gada, duka a cikin rana guda, a Iran. Ba a ga rana irinta ba!!!"
"Ku buɗe wannan Mashigar fa, ku mahaukatan banza, in ba haka ba za ku kasance cikin balbalin bala’i - KAWAI KU JIRA" in ji shugaban, sannan ya ƙara da cewa: "Alhamdulillah."
Trump ya ce kuma Amurka ta ceto wani memban ma'aikatan jirgin F-15 “wanda ya ji rauni sosai kuma jarumi daga surƙuƙin tsaunukan Iran."
Ya ce jami'in da aka ceto "kanal ne da ake matuƙar girmamawa," sannan ya ƙara cewa irin wannan aiki "ba a fiye yin irinsa ba saboda haɗari ga rayuka da kayan aiki."
"Hari na biyu ya biyo bayan na farko, inda muka ceto matukin jirgi ido na ganin ido, abin da ba a saba gani ba, mun shafe awanni bakwai a sama a Iran. Wani ABIN MAMAKI na nuna jarumtaka da ƙwarewa daga kowa!" in ji shi.
"Zan yi taron manema labarai tare da sojoji a Ofishin Oval, ranar Litinin da karfe 1:00 na rana," kamar yadda ya ƙara bayyanawa.
Tun da farko Trump ya faɗa a ranar Lahadi cewa Amurka ta ceto wani jami'in soja a cikin "daya daga cikin mafi jarumtakar ayyukan Bincike da Ceto a tarihin Amurka."
Ya bayyana cewa jami'in ya ji rauni, Trump ya ce zai "warke lafiya."
Ya ce aikin ya biyo bayan wani ceto na daban na wani matukin jirgin Amurka a ranar Juma'a, wanda ba a sanar da shi da wuri ba don kada a yi ƙafar angulu ga aikin na biyu.
Tashin hankali a yankin ya ƙaru tun lokacin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da wani farmaki tare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya kashe sama da mutane 1,340 zuwa yanzu, ciki har da tsohon jagoran addini na ƙasar Ali Khamenei.
Tehran ta mayar da martani da harin jiragen sama marasa matuka da harin makamai masu linzami a kan Isra'ila, haka nan kan Jordan, da Iraki, da ƙasashen Gulf da ke masaukin kadarorin sojin Amurka. Iran ta kuma takaita zirga-zirgar jiragen ruwa ta hanyar Mashigar Hormuz.