Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta ce a ranar Talata ta harbo jirgin yaki mara matuƙi na Amurka MQ-9, tare da cewa wani jirgin RQ-4 da kuma jirgin yaki F-35 su ma sun shiga sararin samaniyar Iran kafin daga bisani su ja da baya.
IRGC ta ce jiragen sun shiga sararin samaniyar Iran ne a yankin Tekun Gulf, kamar yadda wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran ƙasar IRNA ya ruwaito.
Rundunar ta kuma ce tana da haƙƙin “mayar da martani ga duk wani keta yarjejeniyar tsagaita wuta da sojojin Amurka masu kai hari suka yi.”
A baya a ranar Talata, kamfanin dillancin labarai na kusa da gwamnati Fars News Agency ya ruwaito cewa jiragen Amurka da na Isra’ila sun kai hari kan jiragen ruwa na Iran a kudancin tsibirin Larak kusa da Mashigar Hormuz, inda aka kashe “wasu ‘yan ƙasar Iran.”
Ba a iya tabbatar da waɗannan ikirari daga tushe mai zaman kansa ba.
Wadannan abubuwa na faruwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin sasanci ƙarƙashin jagorancin Pakistan domin kawo ƙarshen rikicin da ya fara bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda daga bisani Iran ta mayar da martani a kai.
Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki ne a ranar 8 ga Afrilu, sannan daga baya shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsawaita ta ba tare da sanya wa’adin ƙarewa ba.
A wani bangare kuma, jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce ƙasashen yankin ba za su ci gaba da zama garkuwa ga sansanonin sojin Amurka ba, a cikin wata sanarwa da gidan talabijin na ƙasar ya wallafa ranar Talata.
“Abin da ya tabbata shi ne cewa ba za a mayar da hannun agogo baya ba, kuma al’ummomi da ƙasashen yankin ba za su ƙara zama garkuwa ga sansanonin Amurka ba,” in ji Khamenei, wanda bai fito bainar jama’a ba tun bayan hawansa mulki a watan Maris, cikin saƙon bikin Sallar Layya.
Ya kuma ce Amurka “ba ta da wani mafaka mai aminci a yankin domin kai hare-hare da kafa sansanonin soja, kuma tana ƙara nisa daga matsayinta na baya a kowace rana.”
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce Tehran da Washington sun cimma fahimta kan batutuwa da dama yayin tattaunawa kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin, amma ta yi gargadin cewa har yanzu ba a kusa cimma cikakkiyar yarjejeniya ba.
A ranar Litinin, rundunar US Central Command ta ce sojojinta sun kai hare-hare kan wuraren harba makamai masu linzami a kudancin Iran da kuma wasu kwale-kwalen da ake zargin suna ƙoƙarin dasa nakiyoyi, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta.












