AU ta buƙaci a kwantar da hankali a Sudan ta Kudu yayin da mutum 180,000 suka rasa muhallansu

Ministan Yada Labarai na Sudan ta Kudu Ateny Wek Ateny ya yi watsi da zarge-zargen cewa gwamnati na kai hari kan fararen hula.

By
AU ta bukaci a kwantar da hankula a sudan ta Kudu, yayin da rikici ya raba fiye da mutum 180,000 da mahallansu / AFP

Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ya yi kira da a gaggauta samar da kwanciyar hankali tare da bin ka’idojin yarjejeniyar zaman lafiya ta Sudan ta Kudu na 2018 , yayin da sabon fada ta barke a Jihar Jonglei wanda ya raba mutane fiye da 180,000 da muhallansu, tare da haifar da fargabar sake kai hare-hare kan fararen hula.

A wata sanarwa da aka fitar, Shugaban Kungiyar ta AU Mahmoud Ali Youssouf ya ce ya yi matukar damuwa game da yanayin tabarbarewar tsaro a sassan Sudan ta Kudu, musamman a Jonglei, inda tashin hankali da kalaman batanci suka jefa fararen hula—ciki har da mata da yara—cikin mawuyacin hali.

Hukumomin Sudan ta Kudu sun kiyasta cewa adadin wadanda suka rasa muhallansu a Jonglei ya zarce mutum fiye da 180,000, kamar yadda hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta bayyana a makon da ya wuce.

"Shugaban AU ya matukar kaɗuwa da rahotannin kalaman batanci da wasu ayyukan da ka iya haifar da karin tashin hankali da kuma sanya fararen hula, ciki har da mata da yara, cikin mawuyacin hali," in ji sanarwar.

Youssouf ya yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka sun saba wa ka'ida da tanadi na Yarjejeniyar da aka farfado da ita kan warware rikice-rikice a Jamhuriyar Sudan ta Kudu, kuma ya yi Allah wadai da duk wani kira ko ayyukan tashin hankali kan fararen hula.

Rage tashe-tashen hankula

Ya bukaci dukkan bangarorin da su yi taka tsantsan, kana su rage tashe-tashen hankulan da ake fuskanta nan take, sannan su bi dukkan ka’idojin yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin da aka cim ma da raba iko a karkashin yarjejeniyar.

"Kare fararen hula shi ne babban jigo da nauyi da suka rataya kan dukkan bangarorin," in ji sanarwar, inda ta kara da cewa AU za ta ci gaba da aiki tare da Hukumar Raya Kasa ta Tsakiya (IGAD), da Majalisar Dinkin Duniya, da kuma abokan hulda na ƙasa da ƙasa don tallafawa zaman lafiya da sulhun ƙasa a Sudan ta Kudu.’’

Ƙazalika kiran ya biyo bayan sanarwar da Rundunar Tsaron al’ummar Sudan ta Kudu (SSPDF) ta bayar, inda ta umarci fararen hula, ƙungiyoyin agaji, da ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya da su fice daga yankunan Jonglei da 'yan adawa ke iko da su kafin wani babban aikin soji da ake shirin yi.

"An ba dukkan ƙungiyoyi masu zaman kansu da ma'aikatan UNMISS da ke aiki a gundumomin Nyirol, Uror da Akobo awanni 48 su bar wuraren," kamar yanda mai magana da yawun rundunar SSPDF, Manjo Janar Lul Ruai Koang ya bayyana a wani jawabi na bidiyo da aka fitar ranar Lahadi, yana mai bayyana shirin kai hari "Operation Dorewa Zaman Lafiya" kan dakarun kungiyar 'Yantar da Jama'ar Sudan (SPLM-IO).

Damuwa kan iyakoki

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu (UNMISS) ta nuna damuwa game da umarnin kwashe mutane da kuma wasu rahotanni da ke nuna cewa wani babban soji ya umarci dakarunsa su kai hari kan fararen hula.

UNMISS ta ce yaƙin da ke da alaƙa da rikice-rikice tsakanin manyan bangarorin da aka cim ma yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 ya raba mutane sama da 180,000 da gidajensu a Jonglei.

Ministan Yada Labarai na Sudan ta Kudu Ateny Wek Ateny ya yi watsi da zargin cewa gwamnati na kai hari kan fararen hula, yana mai cewa aikin tsaro a arewacin Jonglei ya “halatta kuma wajibi” don dakatar da ayyukan 'yan tawaye, da dawo da zaman lafiya da kuma kare rayuka da dukiyoyi.

“Ƙasar ba ta cikin yaƙi,” kamar yadda Ateny ya shaida wa manema labarai a Juba. “Muna dakatar da wanzuwar ayyukan dakarun adawa ne kawai, in ji shi.”

Rikicin shekaru masu yawa

Sudan ta Kudu, wacce ta sami 'yancin kai daga Sudan a shekarar 2011, ta sha fama da rikici tun lokacin da yakin basasa ya barke a watan Disamba na 2013 bayan da Shugaba Salva Kiir Mayardit ya kori mataimakin shugaban ƙasa na wancan lokacin Riek Machar, yana mai zarginsa da shirya juyin mulki.

Duk da cewa an cim ma yarjejeniyar zaman lafiya a 2018 da 2022, ana ci gaba da fuskantar rashin zaman lafiya a kasar.

Faɗa ta tsananta tun daga karshen Disamba a Jonglei, inda rikici tsakanin sojojin gwamnati da kuma wadanda ke biyayya ga Machar, wanda ke tsare a gida tun daga Maris na 2025 kana yake fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da cin amanar kasa da laifukan cin zarafin bil'adama.

Tashe-tashen hankula a cikin gwamnatin haɗin kan ƙasa ta rikon kwarya ya kara tsananta, inda aka yi ta samun rahotanni rikice-rikice a farkon wannan shekarar a wasu sassan ƙasar.

Ƙungiyoyin agaji sun yi gargaɗin cewa takunkumin hana shiga ƙasar da rashin tsaro na kawo cikas wajen isar da agaji. Kungiyar Likitoci ta (MSF) ta ce katsewar kayayyakin lafiya a Jonglei ya haifar da karancin magunguna, yayin da hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA a makon da ya gabata ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasa matsugunansu ya wuce 180,000.

Tarayyar Afirka (AU) ta ce za ta ci gaba da ba da himma wajen tallafawa hanyoyin tattaunawa da kuma warware rikicin cikin lumana, tana mai kira ga shugabannin Sudan ta Kudu da su sanya muradun al'umma sama da duk wasu abubuwan da za a yi la'akari da su.