Nijeriya ta sassauta dokokin kuɗaden waje, kamfanonin man ƙetare za su iya fitar da duk kuɗaɗensu

Babban bankin Nijeriya ya cire sharaɗin da ya tilasta wa kamfanonin ƙasashen waje ajiye wani kaso na kuɗaɗen shigarsu na ƙetare a ƙasar na wucin-gadi, lamarin da ya ba su damar fitar da duk kuɗaden shigarsu.

By
Nijeriya ta nemi ta sassauta dokar kuɗaɗen ƙetare a wani ƙoƙari na janyo ƙarin zuba jari. / Reuters / Reuters

Babban Bankin Nijeriya ya cire sharaɗin da ya tilasta wa kamfanonin man ƙasashen waje ajiye wani kaso na kuɗaɗen shigarsu na ƙetare cikin ƙasar na wucin-gadi, lamarin da yanzu zai ba su damar fitar da duk kuɗadensu a wani yunƙuri na inganta hada-hadar kuɗi da kuma aminci a kasuwar kuɗaɗen ƙetaren ƙasar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar 25 ga watan Maris, babban bankin ya ce ya soke sharaɗin na "tara kuɗi " wanda ya bai wa bankuna da aka bai wa izinin dillanci su tura rabin kuɗin fitar da mai ƙetare nan-take, inda za a riƙe sauran kuɗin har zuwa kwanaki 90.

A ƙarƙashin sabon umarnin, kamfanonin mai za su iya fitar da duk kuɗaden da suka samu ta hanyar bankuna da aka bai wa izini, idan sun rubuta kuma suna ba da rahotanni na wata wata, nan-take.

Matakin ya nuna ƙarin saussata kasuwar kuɗaɗen ƙetare ta Nijeriya ga kamfanoni masu fitar da mai, wata muhimmiyar hanyar samun daloli na shigar ƙasar, duk da cewa da ƙyar ne idan hakan zai ƙara samun kuɗi ga ƙasar nan-take.

Wani ɓangare na 'sassauta' kasuwar mai

Babban bankin ya ce matakin wani ɓangare ne na garambawul da ake yi domin “sassauta da kuma ƙarfafa kasuwar bisa halin kasuwa na yanzu,” yayin da take ƙoƙarin daidaita kuɗin naira da kuma janyo masu zuba jari.

Ga kamfanonin man ƙetare, garambawul ɗin ya mayar musu da ƙarin iko kan yadda za su yi da kuɗaden shigarsu, inda ya ba su damar yanke hukunci kan lokaci da kuma yadda za su iya amfani da kuɗaden shigarsu daga ƙetare ba tare da wani lokaci na ajiye kuɗi na dole ba.

Shugabannin kamfanoni sun ce ƙarin damar samun kuɗaɗen shiga na dala yana ƙara ingancin asusu da kuma ƙara rage haɗari a ɓangaren haƙo ɗanyen man Nijeriya, inda aminci game da iya tafiya da uwar kuɗi ke da muhimmanci.

Sauyin ya cire takunkumin da aka ƙaƙaba a watan Fabrairun shekarar 2024 lokacin da dala ta yi ƙaranci sosai, lamarin da ya tura darajar naira ƙasa zuwa wani matakin da ba a taɓa gani ba.

A wancan lokacin, babban bankin Nijeriya ya hana kamfanonin man ƙasar fitar da abin da zarce kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen shigarsu na ƙetare, inda za a riƙe sauran a cikin ƙasar na kwanaki 90 domin tallafa wa samun kuɗin dala a cikin ƙasar.

Farashin yadda kasuwa take

Matakin na farko wani ɓangare ne na wasu jerin gyare-gyare da suka biyo bayan shekarun da aka shafe ana fama da matsin kuɗaɗen ƙetare da aka alaƙanta da ƙarancin farashin mai da kuma matsalar annobar korona.

Tun wancan lokacin, babban bankin ya kuma ƙara kuɗin cinikin dalar domin janyo masu zuba jari da kuma soke ƙayyade farashin dala a kasuwar musayar kudin ƙasar yayin da take cire takunkumin da aka ƙaƙaba a lokacin matsi.