| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
NAFDAC ta haramta kai magunguna Sabon Gari da Niger Street a Kano
Hukumar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin daƙile yaduwar jabun magunguna haka kuma duk kamfanin da ya yi kunnen-ƙashi zai iya rasa lasisinsa.
NAFDAC ta haramta kai magunguna Sabon Gari da Niger Street a Kano
An daɗe ana zargin masu sayar da magunguna a Sabon Gari da Niger Street da sayar da jabun magunguna da kuma amfani da wuraren domin ɓoye jabun magunguna. / Hoto: Getty Images / Others

Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta bayar da umarni ga manyan kamfanonin da ke haɗa magunguna da masu sayar da su kan sari da su daina kai magunguna Kasuwar Sabon Gari da Niger Street da ke Birnin Kano.

Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce hakan ya biyo bayan umarnin da kotu ta bayar na ƙarshe wanda ya ce masu sayar da magunguna su tashi daga Sabon Gari da Niger Street zuwa yankin Dangwauro da ke wajen Kano.

Hukumar ta yi gargaɗi kan cewa duk wani kamfanin da aka kama yana kai magunguna a Sabon Gari Ko Niger Street maimakon Dangwauro wanda nan ne halastaccen wurin da gwamnati ta amince da shi, zai iya rasa lasisinsa.

NAFDAC ta gargaɗi masu shagunan sayar da magunguna da asibitoci da su kula da wannan gargaɗin da ta yi.

Hukumar ta jaddada cewa ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa an daƙile yaɗuwar jabun magunguna ko kuma waɗanda ba su da nagarta.

An daɗe ana zargin masu sayar da magunguna a Sabon Gari da Niger Street da sayar da jabun magunguna da kuma amfani da wuraren domin ɓoye jabun magunguna.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Afirka ta sami tallafin $900m domin faɗaɗa fasahar girki na zamani mara gurɓata muhalli
Rasha na son ƙarfafa alaƙa da Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) - Lavrov
Sojojin Sudan sun ƙwace ƙauyen Al-Kurmuk bayan arangama da dakarun RSF
Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu sun kama masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba fiye da 200
Ƙawancen tsaro na Turkiyya da Afirka na haɓaka a tsarin duniya da ke sauyawa
Jami’an leken asiri sun lalata yunƙurin ‘yan ta’addan Daesh na kai hari a garuruwan Morroco bakwai
'Yansandan Afirka Ta Kudu sun ce mutuwar ɗan Nijeriya ba ta da alaƙa da tashin hankalin ci-rani
MDD ta yi gargaɗin cewa hare-haren RSF na iya mayar da birnin Al-Obeid na Sudan kamar Al-Fasher
Rikicin diflomasiyya ya kaure tsakanin Ghana da Afirka ta Kudu kan mutuwar ɗan Ghana
Burkina Faso, Mali da Nijar sun gabatar da sanarwar ficewa daga ICC, in ji kotun
Sojojin Mali sun raka motocin dakon mai da abinci 940 zuwa Bamako saboda fargabar harin ta'addanci
Sojojin Burkina Faso sun ce sun kashe 'yanta'adda fiye da 400 a wani hari da suka daƙile
An gurfanar da ɗalibai mata takwas a kotu a Kenya kan zargin kisan abokan karatunsu a gobara
Yadda Nijeriya ke fama da hauhawar farashin gas din girki
MDD ta yi gargaɗin cewa cutar Ebola na iya jefa kusan mutane miliyan 1 cikin talauci a DRC
Afirka ta Kudu ta mai da fiye da mutum 25000 kasashensu kafin wa'adin 30 ga Yuni na masu ƙyamar baƙi
Yadda abinci ke yin kisan mummuƙe a Afirka
Burkina Faso ta kawo ƙarshen dangantakar diflomasiyya da Faransa
Fiye da mutum 1,400 sun tsere daga jihar North Darfur ta Sudan a yini ɗaya yayin da ake zafafa yaƙi
Nijeriya da ƙasashe 4 sun ƙaddamar da sabuwar hukuma kan hanyar Abidjan zuwa Lagos ta $16bn