| Hausa
DUNIYA
5 MINTI KARATU
Falasdinawan da suka mutu a yaƙin Gaza sun kai 29,000 — Ma'aikatar Lafiya
Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 136 — inda zuwa yanzu ya kashe aƙalla Falasɗinawa 28,985 tare da jikkata wasu 68,883.
Falasdinawan da suka mutu a yaƙin Gaza sun kai 29,000 — Ma'aikatar Lafiya
Injured Palestinians, including children, are brought to Al Aqsa Martyrs Hospital for treatment following the Israeli attacks in Deir al Balah, Gaza on February 18, 2024. / Photo: AA / AA

1011 GMT — Falasdinawan da suka mutu a yaƙin Gaza sun kai 29,000 — Ma'aikatar Lafiya

Isra'ila ta kashe aƙalla Falasɗinawa 29,092 tare da jikkata wasu 69,028 a yaƙin da take yi a Gaza, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu a yankin da aka yi wa ƙawanya ta ce.

Kazalika, ma'aikatar ta ce Falasɗinawa 107 aka kashe a hare-haren saman da Isra'ila ta kai cikin awa 24 da suka wuce kawai.

0846 GMT — Isra’ila na yi wa Falasɗinawa barazanar kai musu hari a watan Ramadana

Isra’ila ta yi wa Falasɗinawa barazanar kai musu hari a Rafah da ke Gaza idan aka soma azumin watan Ramadana.

Isra’ilar ta ce za ta yi haka ne idan Hamas ba su saki sauran ƴan Isra’ilar da ke tsare a hannnunsu ba.

Yayin da yiwuwar tattaunawar sulhu ke neman dusashewa, Amurka da sauran gwamnatoci, gami da Majalisar Dinkin Duniya, sun kara yin kira ga Isra'ila da ta dakatar da kai farmakin da take shirin kaiwa a Rafah.

Gwamnatin Isra'ila ta ce birnin da ke kan iyakar Masar shi ne wuri mai karfi na karshe da ya rage a Gaza na kungiyar Hamas ta Falasdinu.

0753 GMT — Falasɗinu za ta bayar da shaida a gaban Kotun Duniya

Ƙasar Palestine za ta zama ƙasa ta farko cikin ƙasashe 52 da za su yi magana a Kotun Duniya yayin da kotun za ta shafe kwana shida tana sauraren ƙarar da aka shigar a gabanta.

“Muna so mu ji sabbin kalamai daga kotun” in ji Omar Awadallah, shugaban sashen Majalisar Ɗinkin Duniya a Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasɗinu, gabannin soma sauraren ƙarar.

“Akwai buƙatar su yi la’akari da batun kisan kiyashi a koken Afirka ta Kudu,” kamar yadda ya bayyana inda yake bayani dangane da wani koken na daban da ke gaban kotum. “A yanzu muna so su yi la’akari da batun wariyar launin fata.”

0150 GMT — Isra'ila ta dage kan kai hari Gaza da 'nufin korar mutane ƙarfi da yaji'

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya ce Isra'ila ta dage kan ci gaba da kai hare-hare a Gaza domin korar mutane da raba su da muhallansu, musamman a birnin Rafah.

"Gwamnatin Isra'ila da sojojinta na ci gaba da kai hare-hare a garuruwa daban-daban na Gaza, musamman Rafah da nufin korar 'yan ƙasar ta ƙarfi da yaji. Ba za mu amince da hakan ba, haka kuma 'yan'uwanmu da ma duniya baki daya ba za su amince ba," ya faɗa a wani taro na gwamnatin Falasdinu da aka gudanar a Ramallah, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA.

Ya jaddada cewa halin da ake ciki a Rafah ya zama mai matuƙar haɗari da wahala, yana bukatar gwamnatin Falasdinu ta dauki matakin gaggawa.

Ya kara da cewa sun hallara ne domin tattaunawa kan lamarin domin hana ci gaba da kai hare-hare da kuma hana Isra'ila korar Falasdinawa daga yankunansu da kuma kasarsu.

0133 GMT — WHO ta taimaka wajen kwashe marasa lafiya 14 daga Asibitin Nasser da ke Gaza da aka yi wa ƙawanya

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta taimaka wajen kwashe majinyata 14 daga Asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis a kudancin Gaza, wanda sojojin Isra'ila ke yi wa ƙawanya, in ji Ma'aikatar Lafiya ta Gaza.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce an kai marasa lafiyan, wadanda suka hada da biyar da aka yi wa wankin ƙoda da uku da ke cikin tsananin kulawa, zuwa asibitocin da ke kudancin kasar, sakamakon kokarin da hukumar ta WHO ta yi.

Ta ce ana ci gaba da matsa lamba kan Isra'ila ta kwashe dukkan majinyata daga asibitin, wanda ta mayar da shi barikin soji bayan katse wutar lantarki da kuma hana na'urorin iskar oxygen aiki.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda