| Hausa
WASANNI
3 MINTI KARATU
Koci uku a Turai da za su bar kulob ɗinsu a ƙarshen kakar bana
Zuwa yau, manyan koci guda uku na manyan ƙungoyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Turai sun sanar da aniyarsu ta barin jagorancin ƙungiyoyin nasu a tsakiyar shekara bayan kammala kakar wasa ta bana.
Koci uku a Turai da za su bar kulob ɗinsu a ƙarshen kakar bana
Tuchel Xavi Klopp / Others

Yayin da ya rage kusan wasanni 12 a kakar bana ta gasar ƙwallon ƙafar ƙwararru na yawancin ƙasashen Turai, rahotanni sun tabbatar da cewa koci guda uku za su bar kulob ɗin da suke jagoranta a ƙarshen kakar wasannin ta bana.

A Ingila, tun a watan Janairu ne kocin Liverpool Jorgen Klopp ya sanar da cewa a ƙarshen kakar bana zai bar kulob ɗin da ya kwashe shekaru tara yana jagoranta.

A karkashin Klopp, Liverpool ta lashe kofin Firimiya da kofin Zakarun Turai na UEFA, da kofin FA. Sannan ya ciyo wa Liverpool kofin UEFA Super Cup, da kofin FIFA Club World Cup.

Yayin sanar da aniyarsa ta barin Liverppol, Klopp ya bayyana cewa zai ɗauki hutun shekara guda daga aikin jagorancin kulob ɗin ƙwallo, sannan ba zai karɓi aikin jagorantar wani kulob ba a Gasar Firimiya ta Ingila.

A Sifaniya kuwa, Xavi Hernandez na Barcelona zai sauka daga muƙaminsa na manajan kulob din na Laliga da zarar ana kammala wasannin wannan kakar bana a watan Yuni mai zuwa.

Duk da cewa Xavi Hernandez ya ciyo wa Barcelona kofin LaLiga na bara, kocin wanda tsohon mashahurin dan wasan kulob din ne, ya sanar cewa yana ji kamar zai ajiye kwallon magwaro ne.

Xavi ya ƙara da cewa "Kullum ana sa mutum ya ji kamar ba ya yin kokari”, wannan ne ya sa yake farin cikin barin kulob din.

A kasar Jamus a gasar Bundesliga kuwa, Thomas Tuchel, wanda Bajamushe ne zai bar jagorancin kulob din Beyern Munich a karshen kakar bana, kamar yadda kulob din ya sanar a makon da ya gabata.

Tuchel ya ciyo wa Bayern kofin Bundesliga a bara, amma a wannan kakar labarin ba ya masa kyau. A yanzu Bayern tana da maki 53 ne kacal bayan buga wasanni 23, inda take bayan Bayer Leverkusen da maki 8.

Kocin Leverkusen dan kasar Sifaniya, Xabi Alonso, yana cikin manyan kocin da ake gani za su iya maye guraben da wadannan koci guda uku za su bari.

Shi dai Alonso ya fara zama koci da sa'a a ƙungiyar ta Leverkusen, inda zuwa yau ba a taba yin nasara kan kungiyarsa ba a kakar bana, cikin dukkanin gasanni.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
An dakatar da Cristiano Ronaldo na tsawon kwana 30 da cin sa tarar €255 kan barin sansanin Portugal
Istanbul ta cika da ɗoki da karsashi gabanin wasan Galatasaray da Barcelona a Gasar Zakarun Turai
Hukumar ƙwallon ƙafar Portugal ta dakatar da Ronaldo daga buga wa ƙungiyar ƙasar wasa
Messi da 'yanwasan Argentina sun mana wulakanci, "sun hana mu jesi da yin hoto", in ji kocin Benin
Arda Guler ya tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid zuwa 2031
Ronaldo zai iya komawa tawagar Portugal idan yana so, in ji kocin ƙasar
Tirkashi: Real Madrid na so a ƙwace wa Barcelona kofuna 9, ta gabatar da ƙorafi mai shafi 50,000
Shugaban hukumar ƙwallo da kocin Portugal sun zauna don lallashin Ronaldo bayan ƙin saka shi a wasa
Barcelona ta fusata da Ancelotti kan raunin da Raphinha ya samu a wasan Brazil da Australia
An samu Manchester City da laifin keta dokokin kuɗi
Nijeriya da Ghana sun sha kashi a wasannin neman gurbin shiga Gasar AFCON ta 2027
Manyan kulob sun shirya wawason 'yanwasan Man City idan kotu ta kore ta daga Gasar Firimiya
Zidane ya yaba wa Turkiyya gabannin wasansa na farko a matsayin mai horar da tawagar Faransa
Taiwo ya maye gurbin Osimhen yayin da aka buɗe sansanin horaswa na Super Eagles
Kocin Super Eagles ya fitar da sunayen ‘yanwasan da za su buga wasanni a Satumba da Oktoba
Messi ya ci ƙwallonsa ta 100 a Inter Miami yayin da suka lashe Kofin Campeones
Mbappe ya ce ya ƙi sa rigar Ceuta yadda ya kamata ne don tausaya wa baƙin haure 'yan Morocco
Messi na shirin buga wa Argentina wasansa na ƙarshe
Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya