Fasa ƙwaurin abinci: Sabon ƙalubalen da ke gaban Nijeriya a yayin da abinci ke ƙara tsada
Ayyukan masu fasa ƙwaurin abinci daga Nijeriya zuwa ƙasashe maƙota ya ta'azzara matsalar hauhawar farashin abinci a ƙasar, daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin toshe ɓarakar da ke iyakokin ƙasar.
Daga Abdulwasiu Hassan
Rahotanni na cewa motoci maƙare da hatsi da sauran kayan abinci na fitar da kayan abinci ta ɓarauniyar hanya daga jihohin Nijeriya zuwa ƙasashe maƙota, duk da cewa 'yan Nijeriya na fama da matsalar masu ɓoye abinci da kuma tashin farashin kayan abincin.
Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya fito fili ya bayyana yadda girman matsalar fitar da abincin take, a wajen wani taro a Abuja, ranar 20 ga Fabrairu.
“A kwanaki uku da suka gabata kawai, an kama manyan motoci 45 maƙare da masara, a kan hanyarsu ta fita zuwa ƙasashe maƙota,” a cewar Shettima a wajen taron.
“Daga lokacin da aka kama waɗannan motocin kayan abincin, farashin buhun masara ya faɗi da N10,000… Akwai wasu miyagu da suka dage wajen yi wa ƙasarmu zagon ƙasa.”
Kafin Mataimakin Shugaban ƙasar ya yi maganar a wajen taron, hukumar hana fasa ƙwauri ta ba da rahoton kama motoci maƙare da kayan abinci da wasu masu fasa ƙwauri suke ƙoƙarin fitar da su ta hanyoyi da dama, da suka haɗa da wasu a jihar Jigawa ta arewa maso yammacin ƙasar.
Ba a faye jin hukumar ta hana fasa ƙwauri tana kama abincin da ake fita da shi ta kan iyakoki ba. Babban aikinta shi ne hana shigo da wasu nau’ukan kaya zuwa ƙasar, kamar shinkafa, don tabbatar da manufar gwamnati ta bunƙasa noma a cikin gida.
In ban da a ‘yan shekarun nan, babban ƙalubalen Nijeriya shi ne daƙile masu fasa ƙwaurin man fetur mai rangwame zuwa ƙasashen ƙetare, sakamakon tallafin gwamnati kan farashinsa.
Lokacin da hukumomi suka gaza daƙile fitar da man zuwa ƙasashe maƙota, sai suka rufe iyakar da ke Seme, tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Benin a 2019.
Wannan mataki na da manufar kare manoman shinkafa na cikin gida da masu sarrafa ta, daga barazanar shinkafar da ake shigo wa da ita ta iyakar Benin.
A cewar gwamnati, wannan mataki na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa aka janye tallafin man fetur, abin da kuma ya haifar da wasu sabbin matsaloli.
A yanzu Nijeriya na yaƙi da mummunan tashin farashin kayan abinci, wanda Hukumar Ƙididdiga ta Kasar ta ce ya kai kashi 35.41% a watan Janairu.
Ƙasar na ɗaukar matsanantan matakai don rage tashin farashin abinci, amma wani ƙalubale ne mai girma.
Matakan gyara
Nijeriya ta sauya daga tsarin ƙayyade darajar Naira zuwa tsarin barin ta ta yi gogayya a kasuwar canji domin kuɗin ya samu "darajarsa ta ainahi". Wannan, gami da cire tallafin man fetur sun zama manyan sauye-sauyen da shugaba Bola Tinubu ya ayyana lokacin da ya karɓi aiki a watan Mayun bara.
Sauyawa zuwa tsarin sakin Naira ta yi gogayya ya haifar da karyewar darajar kuɗin ƙasar daga kusan 450 ga kowace dalar Amurka, zuwa kusan 1,500 a kasuwar canjin ƙasar.
Sakamakon wannan karyewar darajar kuɗin Nijeriya, kuɗin kasashe rainon Faransa na CFA wanda maƙotan Nijeriya ke amfani da shi yanzu ya samu daraja sama da ta Naira.
Wannan ya janyo tsadar ayyukan fasa ƙwaurin kayan abinci daga wasu ƙasashen zuwa Nijeriya, kuma ya janyo samun riba ga manoman abinci na Nijeriya su sayar da shi a kasuwannin waje.
Masana sun ce wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa jami'an hukumar hana fasa ƙwauri suke yawan kama motoci maƙare da abinci da ake shirin fitar da shi waje.
Mutuwar kasko
Duk da cewa yunƙurin gwamnati na adana kuɗaɗen waje da take samu yana yin aiki, a ɓangare guda kuma yawan 'yan ƙasar na fama da matsananciyar tsadar rayuwa.
Shugaba Tinubu ya ce yana sane da cewa sauye-sauyen da ake yi suna haifar da wahalhalu ga 'yan ƙasa, amma ya yi alƙawarin cewa wahalar za ta zama ta ɗan wani lokaci.
"Akwai nasara a gaba. Ni na nemi wannan aikin don haka ba na kokawa kan aikin da ke gabana. Ina ɗaukan duk alhakin da ke kaina," in ji Shugaba Tinubu.
Shugaban ya ba da umarnin fito da hatsi daga rumbunan ajiyar abinci na ƙasar, tare da wasu karin matakan, domin rage tashin farashin kayan abinci.
Hukumomin hana fasa ƙwauri sun fara sayar da shinkafar da suka ƙwace a kan farashi mai rahusa na N10,000 a kan kowane buhu mai nauyin 25kg, don sauƙaƙa wa jama’a. Su ma gwamnatocin jihohi sun ƙaddamar da nasu tsare-tsaren na ba da tallafi don ragewa jama’a raɗaɗi.
Iyakoki marasa tsaro
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana a taron na Abuja cewa a yankin ƙaramar hukumar Illela kaɗai a jihar Sokoto, an bankaɗo haramtattun hanyoyin 32 da ake fasa ƙwauri ta cikinsu.
Za a iya auna girman matsalar ta la’akari da cewa a iyakar Illela wani ɗan ƙaramin yanki ne cikin kilomita 1,600 na iyakoki marasa tsaro tsakanin Nijeriya da Nijar. Ƙasar tana kuma da iyakoki da suka kai na dubban kilomita tsakaninta da Chadi da Kamaru.
Wani hasashe ya ayyana yawan haramtattun iyakokin da ake bi don fasa ƙwauri da cewa sun haura 1,000, abin da ya sa zai yi wahala a ce an toshe su duka.
Akwai masu ganin cewa taƙaita cinikayya ce kawai za ta magance matsalar, duk da cewa wannan dabara da kuma sauran matakan na rufe iyakoki tsofaffin yayi ne, a fagen tattalin arziki na zamanin yau mai ƙara dunƙulewa.
Akwai abubuwan alfanu da dama idan ƙasa tana hulɗar kasuwanci a buɗe cikin hikima. Rashin ba da damar gogayya na mayar da masana’antun cikin gida baya, sannan kuɗin da ake kashe wa wajen sarrafa kaya zai cutar da walwalar jama’ar ƙasa.
Nijeriya za ta iya saukar da farashin kayan abinci ta hanyar bin wasu dabarun cinikayya, soke wasu manufofin tattalin arziƙi da ke ƙara kuɗin sarrafa kaya, da zuba jari a ɓangaren noma, da kuma buɗe ɓangaren zuba jari daga ƙasashen waje.
Wata hanyar kuma ita ce sanya ido a kan harkar musayar kuɗaɗen ƙetare don rage fitar da abinci waje. Fitar da kaya abu ne mai kyau, amma ba ta irin wannan hanya ba.
Murƙushe masu mugun tanadi
Bayan Hukumar Yaƙi da Rashawa da Karɓar Ƙorafi ta jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta fara kai farmaki kan mutanen da ta ce suna ɓoye kayan abinci, Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su ringa bankaɗo masu ɓoye abinci a sauran sassan ƙasar.
“Wannan lokaci ne da za mu haɗa ƙarfinmu waje guda, mu goyi bayan shugabanmu da gwamnatinmu, da kawunanmu. Muna da dukkan abin da ake buƙata, muna da basira, kuma za mu iya sauya al’amura. Muna kan hanyar inganta tattalin arziƙinmu,” a cewar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Ya ce gwamnatinsa za ta bunƙasa noma a yankunan karkara, a matsayin mafari.
“Ya kamata mu ringa cin abin da muke nomawa, sannan mu noma abin da muke ci. Ya kamata mu tunkari wannan ƙalubalen, sannan mu yi amfani da filayen da muke da su, don noma abinci,” a kalaman Sanwo-Olu ga mutanen Legas.