Tauraron ɗanwasan Nijeriya Victor Osimhen, ya ci ƙwallo a bugun ɗurme ya kuma ba da tallafin ƙwallo a wasan da Galatasaray ta doke Kayserispor da ci 4–0, a gasar Super lig ta Turkiyya.
Wannan ƙwallo ita ce ta 200 da ya ci a rayuwarsa ta ƙwararren ɗanƙwallo, wanda wani mataki ne na nasara da ba kowane ɗanwasa ne ke samun wannan ba.
Osimhen ya cim ma wannan gagarumin matsayi a ƙungiyoyi da dama a Turai, inda ya ci ƙwallo 76 a Napoli ta Italiya, 20 a Charleroi ta Belgium, 18 a Lille ta Faransa, da 51 a Galatasaray ta Turkiyya.

A fagen ƙwallon ƙasa-da-ƙasa, Osimhen ya nuna fice a cin ƙwallaye a tawagar Nijeriya. Da ƙwallaye 35, a yanzu shi ne na biyu a yawan ƙwallaye a tawagar Super Eagles, inda da ƙwallo biyu Rashidi Yekini ya wuce shi.
A tarihin ƙwallo a Nijeriya, ‘yan wasa ƙalilan ne suka haura adadin ƙwallo 200. Yekini shi ne wanda ya ci ƙwallo kusan 483 a rayuwarsa, sai kuma Odion Ighalo da ya ci ƙwallo sama da 219 a Nijeriya da ƙungiyoyin da ya buga wa.
Shi ma tsohon ɗanwasan Everton da Portsmouth, Yakubu Aiyegbeni ya yi ritaya yana da ƙwallo 215, ciki har da ƙwallo 95 a gasar Firimiya ta Ingila.
Cewa Victor Osimhen mai shekaru 27 ya kai matakin cin ƙwallo 200 na nufin ya shiga sahun zakarun ‘yanƙwallon Nijeriya, ga shi kuma yana da sauran shekaru a gaba.











