Zimbabwe ta ƙaddamar da sabuwar takardar kuɗin ƙasar
Ƙaddamar da sabbin kuɗin da ake kira ZiG na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar Zimbabwe ke ƙoƙarin shawo kan mummunar hauhawar farashin kayayyaki da kuma daidaita tattalin arzikinta da ke fama da ƙalubale.
Babban bankin ƙasar Zimbabwe ya ƙaddamar da sabbin “tsararrun takardun kuɗi” ranar Juma’a.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ƙoƙarin shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki da kuma daidaita tattalin arzikinta da ya daɗe yana fama da tarin ƙalubale.
"Daga yau…Bankuna za su soma canza ma'aunin dalar Zimbabwe da ake hada-hada da shi zuwa sabon kuɗin, wanda za a kira shi 'Zimbabwe Gold' (ZiG), '' kamar yadda Gwamnan babban bankin ƙasar John Mushayavanhu ya bayyana a yayin da yake gabatar da sanarwar manufofin sabon kuɗin.
Ana sa ran matakin zai samar da ''sauƙi da kuma daidaito a harkokin kuɗin ƙasar," in ji shi.