| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Kotu ta bayar da umarni EFCC ta tsare Emefiele
Hukumar EFCC, mai yaƙi da masu yi wa arzikin Nijeriya ta'annati, za ta ci gaba da tsare Godwin Emefiele zuwa ranar 11 ga watan Afrilu inda kotu za ta yanke hukunci kan bayar da belinsa.
Kotu ta bayar da umarni EFCC ta tsare Emefiele
Ana zargin Godwin Emefiele da laifuka da dama ciki har da almundahana da halatta kuɗaɗen haramun./Hoto:OTHER / Others

Wata Babbar Kotu da ke birnin Lagos na Nijeriya ta bayar da umarni ga hukumar EFCC ta ci gaba da tsare tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele.

Alƙalin Kotun, Mai Shari'a Rahman Oshodi ne ya bayar da umarnin a zaman kotun na ranar Litinin.

Hukumar EFCC, mai yaƙi da masu yi wa arzikin Nijeriya ta'annati, za ta ci gaba da tsare tsohon gwamnan na CBN zuwa ranar 11 ga watan Afrilu inda kotu za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa.

Ana zargin Godwin Emefiele da laifuka 26 ciki har da almundahana da halatta kuɗaɗen haramun.

EFCC ta zargi Emefiele da ajiye kuɗin da ya kusa dala biliyan biyu ba tare da bin doka ba.

Kazalika Alƙalin Kotun, ya bayar da umarni a kai Henry Omoile, wanda ake zargi da haɗa baki da Emefiele wurin tafka almundahana, gidan kurkukun Ikoyi da ke Lagos, shi ma zuwa ranar Alhamis don sauraren ƙorafinsa kan bayar da shi beli.

Tsohon gwamnan na CBN yan fuskantar irin waɗannan tuhume-tuhumea wata kotun da ke Abuja.

A watan Yulin 2023 shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga aiki sannan aka ƙaddamar da bincike a kan ofishinsa da kuma yadda ya tafiyar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Sierra Leone ta amince ta karɓi kashin farko na waɗanda aka taso ƙeyarsu daga Amurka
'Makashin Al Fasher' ya koma fagen daga a yaƙin Sudan: Rahoto
Nijar da China sun cim ma yarjejeniyar mai bayan watanni ana takaddama
Adadin mutanen da suka mutu a Congo saboda kamuwa da Ebola ya kai 131
Kenya ta kama wata mata bisa zargin damfarar Ba’amurke dala 431,000 a yarjejeniyar cinikin zinare
Dole Afirka ta daina bin umarnin manyan ƙasashen duniya
WHO ta bayyana ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Kongo a matsayin 'matsalar lafiya ta gaggawa'
Mutum 80 sun rasu a sabuwar ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Congo
Sojojin Sudan sun ƙwace iko da wani muhimmin birni a kusa da iyakar Habasha bayan arangama da RSF
Yakin Sudan: Yara na daga gomman da aka kashe a arangamar makonni biyu a Kordofan
Nijar na son ƙara adadin jihohinta daga 8 zuwa 19 da kuma sauya sunayen wasu jihohim
Shirin 'Big Catch-Up': Kokarin da ya kawo alluran rigakafi miliyan 100 ga yaran Afirka da aka manta
Ghana za ta kwashe ɗaruruwan 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu bayan hare-haren ƙin jinin baƙi
Bankin Ci-gaban Afirka ya amince da fitar da dala miliyan 61 don tallafa wa mata a Nijeriya
'Yansanda sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da Faransa a taron Afirka-Faransa a Kenya
Shugaban Afirka ta Kudu Ramaphosa zai ƙalubalanci rahoton kwamiti kan rashin ɗa'a
An ceto ‘yan Ghana 28 da aka yi safararsu zuwa Côte d’Ivoire
Dangote na duba yiwuwar gina sabuwar matatar mai a Kenya mai tace ganga 650,000 a kullum
‘Yanta’adda sun kashe aƙalla mutum 70 a Mali a cikin kwanaki biyu
Nijar ta dakatar da kafafen yada labarai na Faransa guda 10