| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Nijeriya ta ƙaddamar da rigakafin sanƙarau irin sa na farko a duniya
Rigakafin zai kare mutane daga "nau'i biyar" na ƙwayar cutar sanƙarau da ake kira meningococcus bacteria , in ji darakta janar na WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Nijeriya ta ƙaddamar da rigakafin sanƙarau irin sa na farko a duniya
Ƙungiyar Gavi da ke fafutukar yi rigakafin cututtuka a duniya ce ta ɗauki nauyin yin rigakafin daga ranar 25 zuwa 28 ga watan Maris da zummar yi wa fiye da mutum miliyan ɗaya ƴan shekara ɗaya zuwa 29 allurar./Hoto: Reuters / Others

Nijeriya ta ƙaddaramar da wani nau'i na rigakafin cutar sanƙarau mai suna Men5CV da "zai kawo sauyi sosai", wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce shi ne na farko a duniya.

Rigakafin zai kare mutane daga "nau'i biyar" na ƙwayar cutar sanƙarau da ake kira meningococcus bacteria , in ji darakta janar na WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.

"Sanƙarau tsohuwar cuta ce mai kisa, amma wannan sabon nau'in rigakafin yana da damar kawo sauyi a kan cutar, zai hana ɓarkewar ta a nan gaba sannan ya kare mutane daga mutuwa," a cewar Ghebreyesus, a saƙon da ya wallafa a shafin X ranar Juma'a.

"Wannan shiri da Nijeriya ta ƙaddamar ya ƙara kusantowa da mu don cim ma burinmu na kawar da sanƙarau daga nan zuwa shekarar 2030," in ji shugaban WHO.

Hukumar WHO ta ce Nijeriya, mai mutane fiye da miliyan 220, tana cikin ƙasashe 26 da suka fi fama da ciwon sanƙarau.

Ta ƙara da cewa mutum 153 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar a jihohin Adamawa, Bauchi, Gombe, Jigawa, Katsina, Yobe, Zamfara tsakanin 1 ga watan Oktoba zuwa watan 11 Maris ɗin da ya wuce.

Ƙungiyar Gavi da ke fafutukar yi rigakafin cututtuka a duniya ce ta ɗauki nauyin yin rigakafin daga ranar 25 zuwa 28 ga watan Maris da zummar yi wa fiye da mutum miliyan ɗaya ƴan shekara ɗaya zuwa 29 allurar.

"Arewacin Nijeriya, musamman jihohin Jigawa, Bauchi da Yobe sun fi fama da ciwon sanƙarau mai kisa," a cewar Ministan Lafiya na Nijeriya Farfesa Muhammad Ali Pate.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Nijar ta zargi Chadi da haɗa baki da Faransa wajen kai mata hari
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba