| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
Zanga-zangar nuna adawa da wariyar launin fata da ƙyamar Musulunci a Faransa
Masu zanga-zangar sun yi tir da ayyukan cin zarafi da ƴan sanda a Faransa suke yi tare da nuna goyon bayansu ga Falasdinu a yayin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali na jinƙai a Gaza.
Zanga-zangar nuna adawa da wariyar launin fata da ƙyamar Musulunci a Faransa
Masu zanga-zangar suna rike da tuta mai rubutun a "dakatar da wariyar launin fata, dakatar da ƙyamar Musulunci" a gangamin nuna adawa na kungiyoyi daban-daban a Paris a ranar 21 ga Afrilu, 2024. / Photo: AFP       / Others

Kimanin mutum 2,000 ne suka taru a birnin Paris don nuna adawa da wariyar launin fata da ƙyamar addinin Musulunci, da kuma cin zarafin da ƴan sanda suke yi a Faransa yayin da suke nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza waɗanda ke fama da matsala da tashin hankali na jinƙai.

Masu zanga- zangar sun riƙe tutar Falasdinu tare da sanya ire-iren tufafi ko lullubi na kasar yayin da suke rera taken adawa da abubuwan da suke faruwa a Gaza a ranar Lahadi.

Kazalika sun baje alluna da ke dauke da rubutun "A daina nuna wariyar launin fata, a daina ƙyamar Musulunci," "Ya'yanmu na cikin hadari,"

"A daina kisan kare dangi a Gaza" da kuma "mu na adawa da mulkin mallaka da yahudawa ke yi."

Manya-manyan kungiyoyin masu ra'ayin riƙau na Yellow Vest na Faransa da kuma 'yan jam'iyyar La France Insoumise (Faransa Unbowed) da kuma baƙaƙen mutane bakin haure ne suka halarci gangamin.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar ƴan asalin Afirka sun nuna adawarsu ta hanyar raye-raye da kade-kade na wakokin cikin gida.

Kazalika jama’a sun rera taken tunawa da wani matashi ɗan asalin Arewacin Afirka da aka harbe har lahira a shekarar da ta gabata a yayin binciken ƴan sanda a kan hanya.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Kasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha: Lavrov