Iran za ta gudanar da tsarin jana’izar Jagoran Addinin Ƙasar da aka kashe Ali Khamenei tsakanin 4 zuwa 9 ga Yuli, a cewar rahotannin kafar watsa labarai ta gwamnatin Iran.
Shirin zai ƙunshi bankwana a Tehran a ranar 6 ga Yuli da kuma a Qom ranar 7 ga watan na Yuli.
A ranar 9 ga Yuli kuma za a binne Khamenei a hubbaren Imam Reza a birnin Mashhad bayan gudanar da al’amuran jana’iza a ranar 8 ga Yuli.
Hare-haren Isra’ila da Amurka ne waɗanda aka fara kai su ranar 28 ga Fabrairu ne suka yi ajalinsa. Hare-haren sun kuma yi ajalin manya kwamandojin soji da dama da jami’an gwamnati.
Pakistan ta shiga tsakani inda aka tsagaita wuta a ranar 8 ga Afrilu, kuma tun daga nan aka ci gaba da yunƙurin cim ma yarjejeniya mai faɗi.













