Kasar Guinea na neman Faransa ta mayar da ƙoƙon kawuna da dama da kayayyakin mutane da tarihi ya nuna cewa sun yi yaƙi da mulkin mallaka a ƙarni na 19, kamar yadda Ma'aikatar Al'adu ta faɗa wa AFP a ranar Alhamis.
An miƙa buƙatar mayar da abuuwan a tsakiyar watan Yuli kuma sun haɗa da ƙoƙon kan Boubacar Biro Barry, shugaba na ƙarshe da ƙabilar Fouta-Djalon, wanda ke cikin yankin Guinea a yau.
An sare kan Barry da wasu mutane uku: ɗansa, ɗan'uwansa da kwamandansa na yaƙi ne a shekarar 1896 bayan yaƙi da Faransawa. Guinea na neman a mayar da duka ƙoƙon kawunan huɗu.
An kuma nemi a mayar da rubuce-rubuce da sauran kayayyaki na Samory Toure, wani soja-mai-wa'azi wanda ya karɓi addinin Musulunci, kuma ya yi yaƙi da rundunonin mulkin mallakar Faransa don kafa daular kansa.
'Su huta cikin daraja'
Baya ga rubuce-rubuce, Guinea na buƙatar a dawo da takobin Toure, da hularsa da babbar rigarsa, kamar yadda Amirou Conte, Daraktan Gidan Tarihi na Ƙasa na Ma'aikatar Al'adu a Konakri, ya shaida wa AFP.
"Jamhuriyar Guinea za ta ɗauki duk matakan da suka dace don tabbatar da mayar da gawarwakin Barry da na abokan tafiyarsa," in ji Ministan Al'adu na Gini, Moussa Moise Sylla, "domin su huta cikin daraja a ƙasar kakanninsu."
Buƙatun sun biyo bayan ƙaddamar da dokoki a Faransa a 'yan shekarun nan waɗanda suka nufi mayar da kayan da aka ƙwace a lokacin mulkin mallaka.
A watan Satumba 2025, Faransa ta mayar da ƙoƙon kai uku na waɗanda suka rasa rayukansu a azabtarwar zamanin mulkin mallaka a Madagascar. Daga cikin ƙoƙon kawunan, ana ganin ɗaya na sarkin Toera ne, wanda sojojin Faransa suka sare masa kai a lokacin kisan kiyashin Ambiky na 1897.
A watan Mayu, majalisar dokokin Faransa ta amince da wata doka don sauƙaƙe mayar da abubuwan da aka sace a lokacin mulkin mallaka.


















