Syria ta ayyana harshen Kurdanci a matsayin 'harshen ƙasa', sannan ta ba Kurdawa haƙƙin 'yan ƙasa

Dokar ta kuma sanya Nowruz a matsayin ranar hutu a hukumance tare da mayar wa Kurdawa haƙƙoƙinsu na ‘yan ƙasa wanda aka ƙace musu a yayin wata ƙidaya mai cike da ruɗani wadda aka gudanar a shekarar 1962.

By
Shugaban Syria Ahmed al Sharaa / Reuters

Shugaban Syria Ahmed al Sharaa ya kafa wata doka a ranar Jumma'a wadda ta ayyana harshen Kurdanci a matsayin "harshen ƙasa" kuma ta ba al'ummar Kurdawa haƙƙokin ƙasa.

Dokar ta kuma sanya Nowruz a matsayin ranar hutu a hukumance tare da mayar wa Kurdawa haƙƙoƙinsu na ‘yan ƙasa wanda aka ƙace musu a yayin wata ƙidaya mai cike da ruɗani wadda aka gudanar a shekarar 1962.

Kamfanin dillancin labaran Syria SANA ya wallafa saƙon a shafinsa na intanet, inda ya ce dokar ta tabbatar cewa Kurdawan Syria “muhimmai kuma halastattun mutanen Syria ne” kuma al’adunsu da karin harshensu “na cikin wani ɓangare na haɗin kai da ba za a iya raba shi da Syria ba.”

Rubutun dokar

Sashe na 1: Ana ɗaukar Kurdawan Syria a matsayin muhimmin ɓangare na jama’ar Syria, kuma al’adunsu da karin harshensu “na cikin wani ɓangare na haɗin kai da ba za a iya raba shi da Syria ba.

Sashe na 2: Ƙasar tana da alhakin kare bambancin al'adu da harsuna kuma tana tabbatar wa 'yan ƙasa Kurdawa haƙƙin kiyaye gadonsu, fasahohinsu, da haɓaka harshensu na uwa cikin iyakar mulkin ƙasa.

Sashe na 3: Harshen Kurdanci ana ɗaukar shi harshen ƙasa kuma ana ba da izinin koyar da shi a makarantu na gwamnati da masu zaman kansu a wuraren da Kurdawa ke da kaso mai yawa na jama'a, a matsayin wani ɓangare na darasin da mutum zai zaɓa ko kuma a matsayin aiki na al'adu da ilimi.

Sashe na 4: Duk dokoki na musamman da matakan da aka ɗauka bayan ƙidayar da aka yi ta jama’a a shekarar 1962 a lardin Al‑Hasakah an soke su. An bai wa duka Kurdawa waɗanda asalinsu ‘yan Syria ne ne da ke zaune a ƙsar ‘yancin zama ‘yan ƙasa, daga ciki har da waɗanda a baya aka ƙwace ikonsu na zama ‘yan ƙasa, inda yanzu suke da cikakken iko.

Sashe na 5: Bikin "Nowruz" (21 ga Maris) an ayyana shi hutu a hukumance a fadin Jamhuriyar Larabawa ta Syria, a matsayin bikin ƙasa.

Sashe na 6: Kafofin watsa labarai na gwamnati da cibiyoyin ilimi ana wajabta musu su rungumi wani harshe na ƙasa mai haɗa kai. Duk wariya ko warewa bisa la'akari da kabila ko harshe an haramta ta a doka, kuma ƙarfafa rikicin kabilanci zai kasance laifi a ƙarƙashin dokokin da ake da su.

Sashe na 7: Ma'aikatun da hukumomin da abin ya shafa za su fitar da umarnin aiwatarwa da suka wajaba domin aiwatar da tanade‑tanaden wannan doka.

Sashe na 8: Wannan doka za a wallafa ta a Jaridar Hukuma kuma za ta fara aiki daga ranar da aka fitar da ita.