Dimokuradiyya ta dawo da ƙarfinta a Somalia bayan shekaru 56
Yankin Banadir na Somalia da ya hada da babban birnin Mogadishu, ya jefa kuri’a a ranar 25 ga Disamba a karon farko na yin zabe kai tsaye bayan shekaru 56.
Daga Abdulkadir Mohamed Nur
Duk da cewa tsarin zaɓen ƙananan hukumomi a Somalia ya fara ne a ranar 25 ga Disamba, wannan ci gaban ya nuna fiye da batun ranar zaɓe kawai.
Wannan ya nuna wani muhimmin lokaci na tarihi wanda ya ba da damar jama'a su shiga zaɓe kai tsaye bayan shekaru da yawa.
Kafin juyin mulkin soja na 1969, an ɗauki Somalia a matsayin ɗaya daga cikin tsarin siyasa mafi dabbaka dimokuraɗiyya a Afirka da jam’iyyu da dama.
Tsakanin 1960 da 1969, ƙasar ta gudanar da zaɓe mai jam'iyyu da yawa kuma na gaskiya, majalisar dokoki ta yi aiki yadda ya kamata, kuma mulkin siyasa ya canza daga hannu zuwa wani hannun cikin lumana.
Muhawarar da aka sake yi a yau kan zaɓe bisa ƙa'idar mutum ɗaya, ƙuri'a ɗaya a zahiri ci gaba ne na tsarin dimokuraɗiyya wanda aka bari ba a kammala ba a farkon lokacin jamhuriya.
Yankin Banadir, wanda ya haɗa da babban birnin Mogadishu, ya shiga zaɓe a ranar 25 ga Disamba a karon farko cikin shekaru 56 ta hanyar jefa kuri’ar jama'a kai tsaye. Wannan zaɓen ya fito fili ba a matsayin zaɓen gama gari na gida ba kawai, har ma a matsayin mataki na farko da aka ɗauka don ƙarfafa wakilcin dimokuraɗiyya a Somalia.
Wannan matakin ya nuna jajircewar Somalia ga tsarin zaɓe bisa ƙa'idar mutum ɗaya, ƙuri'a ɗaya.
A wannan zaɓen na kananan hukumomi, 'yan takara sama da 1,600 daga jam'iyyu 20 ne suka fafata don wakiltar ra'ayin jama'a a sassa 16 na gudanarwa na ƙananan hukumomi a yankin Banadir.
Yawancin 'yan takarar matasa ne. Wannan hoton ya nuna a fili cewa makomar Somalia yanzu tana samun tsari daga ‘yan kasa matasa masu jini a jiki.
A ranar zaɓen, kimanin ma'aikatan zaɓe 5,000 da aka horar sun yi aiki a cibiyoyin zaɓe, yayin da aka tura jami'an tsaro 10,000 a lokaci guda don tabbatar da cewa an gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali, lafiya da tsari.
Waɗanda ke aiki a rumfunan zaɓe da kuma waɗanda suka kaɗa ƙuri'unsu galibi matasa ne 'yan Somalia.
Wannan yanayi ba wai kawai yana nuna sha'awar matasan Somalia game da makomar ƙasarsu ba ne, har ma yana nuna cewa matasa suna da ra'ayin cewa makomar Somalia na hannunsu.
Yadda aka shirya tsarin
Tsawon shekaru 56, ‘yan kasar Somalia ba su iya zaɓar waɗanda za su mulke su da 'yancinsu ba. Bayan juyin mulkin da Siad Barre ya yi a shekarar 1969, rayuwar siyasa ta jam'iyyu da yawa ta ƙare.
Barre ya dakatar da kundin tsarin mulki ya kuma yi mulkin Somalia tsawon shekaru da yawa ta hanyar mulkin mutum ɗaya.
A wannan lokacin, jama'a ba su da wani ta ce, kuma an kori al'ummar Somalia daga tsarin yanke shawara na siyasar kasar.
Wannan lokacin, wanda ya kawo karshe a 1991, bai kawo dimokuraɗiyya ga ƙasa ba. Akasin haka, Somalia ta ruguje gaba ɗaya, kuma ƙasar ta zama sananniya a duk duniya a matsayin cibiyar yaƙin ƙabilu, mayaƙa, yunwa da talauci.
Kowane birni ya faɗa ƙarƙashin ikon ƙabilu, ƙungiyoyi da mayaƙa daban-daban.
A shekarun 2000, yayin da al'ummar duniya ta fara ɗaukar matakai kan Somalia, an kafa gwamnatocin riƙon ƙwarya.
Mafi girma daga cikin waɗannan hanyoyin shi ne tsarin wakilci bisa ƙabilu wanda aka sani da tsarin 4.5, wanda har yanzu ana amfani da shi. An tsara wannan ne a matsayin sulhu na ɗan lokaci don kada Somalia ta wargaje.
Ya zuwa shekarar 2012, kafa Jamhuriyar Tarayyar Somalia da kuma amincewa da kundin tsarin mulki na wucin gadi ya nuna wani muhimmin sauyi. A wannan shekarar, Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya zama daya daga cikin shugabannin farko da suka bayyana manufar kafa gwamnati da kuma sauya sheka zuwa yin zabe kai tsaye.
Duk da haka, barazanar tsaro, musamman wanzuwar kungiyar 'yan ta'adda ta Al Shabaab, ya hana cim ma wannan burin a cikin dan kankanin lokaci.
An dage zaben da ya dogara da ka'idar kuri'a daya mutum daya, wadda aka tsara a shekarun 2016 da 2020 saboda karancin fasaha da rashin jituwa a siyasance.
A tsawon wadannan shekarun, siyasa a Somalia ta fi karkata ga manyan mutane fiye da jama'a. Kasashe daban-daban sun yi amfani da tsarin zabe, kuma akwatin zabe ya zama ba hakki ba, amma an dade ana dage alkawarin magance hakan.
Duk da haka, an gina karfin zabe a hankali mataki-mataki. An kafa kwamitocin zabe, an yi rijistar jam'iyyun siyasa, kuma an kaddamar da ayyukan gwaji a matakin kananan hukumomi.
Bayan sake zaɓen sa a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2022, Hassan Sheikh Mohamud, duk da waɗannan ƙalubalen, ya ƙaddamar da tsarin da ya dogara da zaɓen jama'a kai tsaye a zaɓen ƙananan hukumomi kuma ya nuna ƙudurin da ya ɗauka na faɗaɗa wannan tsarin zuwa zaɓen shugaban ƙasa.
Saboda wannan dalili, zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a yankin Banadir ba tsari ne da ya takaita ga gwamnatocin ƙananan hukumomi kawai ba.
Ana ɗaukar su a matsayin mataki na farko na zahiri a ƙoƙarin Somalia na kawo ƙarshen shiru na fiye da rabin ƙarni na dimokuraɗiyya.
Haka kuma ana ɗaukar su a matsayin ranar da burin jama'a da aka daɗe ana jira ya zama gaske.
Gina makoma
Ainihin sharadin da Somalia za ta gina makoma mai ɗore wa shi ne tabbatar da shigar jama'arta kai tsaye cikin harkokin siyasa.
Zaɓe bisa ƙa'idar mutum ɗaya, kuri’a ɗaya ba wai kawai yana wakiltar 'yancin saka kuri’a a akwatin zaɓe ba ne, har ma yana da muhimmanci ga jama'a ta hanyar ba su damar yin magana kan makomarsu.
Wannan shiga takara na da matuƙar muhimmanci a sauye-sauyen siyasa da zamantakewa na Somalia.
Tsarin zaɓe wanda aka tsara bisa ga ra'ayin jama'a kai tsaye yana taimakawa wajen sake gina alaƙar aminci tsakanin gwamnati da al'umma.
Zaɓe na gaskiya da tafiya da kowane bangare na ƙarfafa sahihancin waɗanda ke kan mulki yayin da kuma suke shimfida harsashin samar da amincewar zamantakewa a cikin yanke shawara ta siyasa.
Ga al'umma da aka daɗe ana ware ta daga hanyoyin yanke shawara, wannan tsari ya bayyana a matsayin hanya mafi inganci don sake haɗuwa da gwamnati.
Wannan sahihancin yana kuma bayar da damar manufofin tsaro su dogara kan tushe mai ƙarfi na zamantakewa.
A yaƙi da ta'addanci, matakan da ƙasar ke ɗauka suna ƙara inganci da dorewa idan aka haɗa su da goyon bayan jama'a. A lokaci guda, shiga cikin siyasa yana ƙarfafa ƙarfin ƙasar a fannoni kamar tattalin arziki, manufofin ƙasashen waje da shugabanci.
A wannan lokacin, ya zama wajibi ga dukkan masu ruwa da tsaki na siyasa, ko a gwamnati ko na adawa, da kuma da'irorin ilimi, su goyi bayan matakan dabbaka dimokuraɗiyya a fili da kuma yanke shawara.
Alamun shiga sabon zamani
Kyakkyawar aniyar siyasa da ta samu goyon baya daga jama'a ce kawai za ta iya ɗaukar Somalia zuwa mataki na gaba.
Saboda wannan dalili, dole ne a kawo karshen zamanin ciniki a ɓoye da kuma yanke shawara kan makomar ƙasar a cikin tanti.
Har zuwa shekaru uku da suka gabata, Somalia ƙasa ce da bama-bamai ke fashewa kusan kowace rana, kuma ta'addanci da tsoro ne suka zama harkokin rayuwar yau da kullum.
A yau, duk da dukkan wani cikas da barazana, musamman daga ta'addancin Al Shabab, nasarorin tsaro da aka samu sun ba wa al'ummar Somalia damar fitowa kan tituna su ji daɗin kada kuri'a kai tsaye a karon farko cikin shekaru 56.
Wannan hoton da ke fitowa fili yana isar da sako mai haske ga 'yan siyasar Somalia. Yanzu jama'a suna son bayyana ra'ayoyinsu, kuma za a ji su ba tare da wani mai shiga tsakani ba.
Jarumtar da 'yan Somalia suka nuna wa waɗanda suka je rumfunan zaɓe na ɗaya daga cikin matakai mafi ƙarfi da za su iya canza makomar Somalia.
A lokaci guda, jami'an tsaro da suka tabbatar da tsaron zaɓe da Hukumar Zaɓen da ta bayar da damar gudanar da zaɓen a cikin yanayi mai kyau ba tare da wata matsala mai tsanani ba, sun cancanci yabo mai girma.
Saboda haka, bai kamata a ɗauki tsarin da ya fara a yankin Banadir a matsayin wanda aka takaita ga zaɓen ƙananan hukumomi kawai ba, sai dai a matsayin alamar sabon zamani da ake sake fasalta dangantakar da ke tsakanin gwamnati da al'umma.
Marubucin, Abdulkadir Mohamed Nur, shi ne Ministan Tashoshin Jiragen Ruwa na Somalia kuma a baya ya yi aiki a matsayin Ministan Shari'a da Ministan Tsaro. Ya kammala karatunsa daga tsangayar Nazarin Kimiyyar Siyasa ta Jami'ar Ankara.
Togaciya: Ba lallai ra’ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra’ayin dab’i na TRT Afrika ba.