| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
Isra'ila ta kashe wani ɗan jaridar Falasɗinu da iyalansa
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 218, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,943 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,572 ne suka jikkata.
Isra'ila ta kashe wani ɗan jaridar Falasɗinu da iyalansa
Isra'ila na ci gaba da kai hari kan fararen hula a Gaza inda take kashe mutane akasarinsu mata da yara. / Hoto: Reuters / Others

1043 GMT — Isra'ila ta kashe wani ɗan jaridar Falasɗinu da iyalansa

An kashe wani ɗan jaridar Falasɗinu a wani hari ta sama da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza, kamar yadda ofishin watsa labarai na gwamnati ya sanar a Gaza.

An kashe ɗan jarida Bahaa Okasha, wanda mai ɗaukar hoto na Al-Aqsa media network, tare da matarsa da ɗansa a wani harin ba da Isra’ila ta kai kan gidansa da ke sansanin gudun hijira na Jabalia.

Aƙalla ƴan jarida 143 ne Isra’ila ta kashe a yaƙin da take yi a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa sama da 35,000 tun daga 7 ga watan Oktoba.

0947 GMT — Hezbollah ta ce ta kai hari kan sojojin Isra'ila da ke kan iyaka

Kungiyar Hezbollah a ranar Asabar ta ce ta kai hari kan wani gini wanda sojojin Isra'ila suka taru a kusa da iyakar Lebanon da ke kudancin ƙasar.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce mayaƙanta sun kai hari kai tsaye kan "wani gini wanda sojoji suke a Metula da makamai masu kyai.

Harin ya kasance "a matsayin martani ga hare-haren da masu tsatsauran ra'ayin Yahudawa suka kai kan ƙauyukan kudanci da gidajen fararen hula, wanda na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai a garin Tayr Harfa," in ji Hezbollah, yayin da ƙungiyar ke magana kan harin na ranar Juma'a wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane biyu.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda