| Hausa
TURKIYYA
2 MINTI KARATU
'Yan sandan Turkiyya sun kama gomman mutanen da ake zargi 'yan ƙungiyar Daesh ne
'Yan sanda sun kai samame a kudu maso gabashin birnin Sanliurfa da lardin Konya inda suka kama mutum 44 waɗanda ake zargin 'yan ta'addan ƙungiyar Daesh ne.
'Yan sandan Turkiyya sun kama gomman mutanen da ake zargi 'yan ƙungiyar Daesh ne
Wannan samamen ya nuna yadda Turkiyya ke jajircewa wurin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar. / Hoto: AA Archive / Others

'Yan sanda a Turkiyya sun kama mutum 44 waɗanda ake zargin 'yan ƙungiyar Daesh ne, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.

An gudanar da samame daban-daban a ranar Talata a kudu maso gabashin birnin Sanliurfa da tsakiyar lardin Konya domin kama waɗanda ake zargin.

Samame na baya-bayan nan da aka kai na daga cikin babban shirin Turkiyya na yaƙi da ta'addanci wanda samame ne da aka kai fiye da dubu ɗaya kan Daesh tun daga 1 ga watan Yunin 2023, inda aka kama sama da mutum 2,000 da ake zargi.

Waɗannan samamen na zuwa ne bayan wani hari da Daesh ɗin ta kai kan wata cocin Italiya, wanda hakan ya ja Turkiyyar ta ƙara matsa ƙaimi domin yaƙi da ta'addanci.

Turkiyya wadda tana daga cikin ƙasashen da suka soma ayyana Daesh a matsayin ƙungiyoyin ta'addanci tun daga 2013, na ci gaba da fuskantar barazana daga ƙungiyar, inda ta kai hare-hare da dama waɗanda suka yi sanadin mutuwar sama da mutum 300 da kuma jikkata da dama.

Haka kuma ƙungiyar ta ƙaddamar da hare-haren ƙunar baƙin-wake aƙalla goma da tayar da bam sau bakwai da kai hare-hare na makami huɗu a ƙasar.

Irin samamen da ƙasar ke kaiwa na nuni da irin sadaukarwar da Turkiyyar ta yi na tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, da tsaron 'yan kasarta da kuma al'ummar duniya baki daya.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Turkiyya na shirin zuba jarin dala biliyan 2 a sufurin sama da na sararin samaniya cikin shekaru uku
Kamfanin Fergani na Turkiyya ya tura tauraron ɗan'adam na gwaji na 6 sararin samaniya
Turkiyya, Qatar da Pakistan da Indonesia za su sanya hannu kan yarjejeniyar masana'antar tsaro
Antalya ya karɓi masu yawon buɗe ido miliyan 14 daga ƙasashen waje duk da ƙalubalen duniya
Spain na shirin sayen jirgin horar da mayaka na Hurjet kirar Turkiyya guda 15: Shugaban TAI
Turkiyya ta haramta wa shafukan sada zumunta yi wa 'yan ƙasa da shekara 15 rijista
Yarjejeniyar tsaro ta Makka ba ta ba da izinin kai hari kan ƙasashe ba - Turkiyya
Turkiyya ta yi wa Nijeriya ta’aziyya kan hatsarin jirgin soji
Shelar Antalya da Turkiyya ke jagoranta ta haɗa ƙasashe 21 a haɗin kan lumana kan sararin samaniya
Emine Erdoğan ta jagoranci kiran matan shugabannin duniya na son MDD tai tsarin kare yara a intanet
Turkiyya za ta ci gaba da magana kan Falasɗinawa: Erdogan
Zauren kotu ya dace da masu aikata laifukan yaƙi ba zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ba: Erdogan
Jami’an Sojin Ruwa 30 na Saudiyya sun kammala karɓar horo a kamfanin tsaron Turkiyya, Baykar
Yadda Turkiyya ke taimaka wa Iraƙi wajen isar da albarkatun manta zuwa kasuwannin ƙasa da ƙasa
An wallafa jawabin Shugaba Erdogan na UNGA-81 a matsayin littafi cikin harsuna uku
Shugaban Turkiyya Erdogan ya buƙaci haɗin ƙan Musulmai, ya soki nuna wariya
Emine Erdogan ta buƙaci a rabu da ‘al’adar jefar da kaya' a koma ga tsarin sabuntawa
Erdogan ya yi kira da a gyara MƊD, ya nemi a soke ikon kujerar na-ƙi
Abincin Afirka daga Turkiyya
Shugaba Erdogan na Turkiyya ya tafi New York taron Majalisar Dinkin Duniya